A ranar Alhamis ce Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano ya bayyana yadda ya tsallake rijiya da baya a hatsarin jirgin cikin 1996, wanda ya kashe Gwamnan Kano na mulkin soja, Abdullahi Wase.
Ganduje na bayanai ne a lokacin da sabuwar Jakadar Najeriya a Romania, Safiya Nuhu ta kai masa ziyasa a gidan gwamnati.
Safiya dai diyar Nuhu ce, wanda shi ma ya na cikin wadanda su ka rasa rayukan su a lokacin da hatsarin jirgin ya faru a Jos, cikin 1996.
“A lokacin ni ina Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri na Jihar Kano. An shirya za mu je garin Wase, mahaifar gwamnan lokacin na Jihar Kano, Abdullahi Wase, domin ganin yadda wani aikin ginin masallacin Juma’a ke gudana a garin Wase da ke cikin Jihar Filato a lokacin.
“Kuma ni ne shugaban shirya gidauniyar tara kudaden ginin masallacin. To Gwamana ya shirya zuwa duba aikin gini, kuma zai yi ta’aziyyar wani dan uwan sa da ya rasu. Ni ne na tsara yadda tafiyar za ta kasance.
“Ni na shirya samo wani jirgi na Aminu Dantata, kuma ni na rubuta sunayen mu da za mu tafi tare da Gwamna.
“Ya kasance mahaifin ki ba ya cikin masu tafiyar. Amma kwana daya kafin tafiyar, a cikin gidan gwamnati ga ni ga shi, sai ya roki ni cewa ya ba a sunan sa cikin masu tafiya ba?
“Wase ya ji mu, sai ya ce a saka sunan sa. Ya ce shi ma ya na so a saka shi cikin tafiyar.
“A lokacin mahaifin ki shi ne Babban Sakatare, Gidan Gwamnatin Jihar Kano.
Ganduje ya shaida wa jakadar cewa daga gidan gwaknati, shi da mahaifin ta kowa ya hau motar sa su ka nufi gidajen su, a unguwar Sharada.
Sai dai kuma bayan Ganduje ya koma gida ne, sai aka sanar da shi daga ofishin sa cewa akwai muhimmin batu ya taso daga Fadar Shugaban Kasa, za su zo duba wani aiki.
“A kan haka ne na yanke shawarar cewa ni ba zan je tafiya zuwa Wase ba. Gara na tsaya ofis na tsara komai, yadda Gwamna Wase na dawowa sai na kai masa takarda kawai ya sa hannu, domin batun masu zuwa daga fadar shugaban kasa daga Abuja.
“Da safe karfe 8 na safe na wuce ofis, ina zaune mu na aiki a ofis, sai aka sanar da ni cewa ana nema na a Gidan Gwamnati. Na yi mamaki, saboda na san gwamna ba ya nan sun yi tafiya.
“Ina zuwa sai na taras da Burged Kwamanda na Kano tare da Kwamishinoni, su kwamishinonin na ta rusa kuka. Na ce hala jirgin ne ya yi hatsari?!
Nan dai babban sojan ne ya sanar da mu cewa jirgin su gwamna Wase ya yi hatsari a Jos, kuma babu ko mutum daya da ya tsira.
“Nan take ya ce mana na ba ku awa daya kowa ya shirya mu dunguma zuwa Jos, domin mu tantance gawarwakin su, a dauko su zuwa gida.”
Ganduje ya shaida wa jakadar cewa shi da mahaifin ta abokai ne, tun a makaranta, har a jami’a da wurin aiki karkashin gwamnatin jihar Kano. Kuma sun yi aiki tare a Babbar Kwalejin Gumel.