Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta cafke wani magidanci mai shekaru 49, William Akpan da laifin yin lalata da ‘yar sa har na tsawon shekaru biyar.
Kakakin rundunar Abimbola Oyeyemi ya sanar da haka a hira da yayi da manema labarai a garin Ogun ranar Litini.
Oyeyemi ya ce’yan sanda sun kama Akpan bayan ‘yar da kanta ta kai karar abin da mahaifinta ya ke yi mata ofishin su dake Itele Ota karamar hukumar Ado-Odo-Ota.
Ya ce yarinyar ta bayyana wa jami’an tsaro cewa mahaifinta ya fara lalata da ita tun tana da shekaru bakwai da haihuwa sannan ya ci gaba da hakan har zuwa yanzu, shekaru biyar kenan.
” Tace ta gaji da biye wa mahaifinta suna lalata ne ya sa ta garzaya ofishin ‘yan sanda domin hukuma ta shiga ciki, abin ya tsaya haka nan.
Bayan haka shine ‘yan sanda suka cafke mahaifin domin tuhumar sa.
Ya ce yayin da ake gudanar da binciken Akpan ya bayyana wa jami’an tsaro cewa ya aikata haka ne saboda matarsa ta yi masa tsufa sannan ya daina sha’awar ta kwata-kwata.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Edward Ajogun ya ce fannin gurfanar da masu aikata laifuka irin haka za ta ci gaba da gudanar da bincike a kai.
Sannan ita ‘yarinyar za a kaita asibiti domin likitoci su duba ta.
Discussion about this post