Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya dauki nauyin ceto wata yar shekara shida bayan ya biya mata kudin magani dungurum da aka yi mata aikin gabanta da matsafa suka illata.
Ita dai wannan yarinya ta faɗa hannun matsafa ne a garin Jama’are inda suka illata gabanta wajen yin wani ƙulumboto na su.
Cikin taimakon Allah gwamnan jihar Bauchi ya wuf ya sa a gaggauta kaita asibiti inda ka yi mata aiki a gabanta kuma yanzu komai ya dawo daidai.
Gwamna Bala ya biya kudin aikin da kula da yarinyar.
Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Jihar Bauchi, Ladan Salihu ya rubuta a shafinsa tare da saka hotunan yarinyar zaune tare da gwamnan.
Yace ” Wannan Yarinya ce da matsafa suka yanke mata al’aura a Karamar Hukumar Jama’are.
” Da yardar Allah Anyi mata aiki kuma ta samu chikakken lafiya.
” Allah ya saka wa Gwamna Bala Mohammed da ya dauki nauyin aikin da aka yi mata.
Allah ya kara mata lafiya.
” Ya kiyaye Al’umma daga wannan da dukkan masifa. Amin.