Yadda gobarar wutar lantarki ta kone kasuwar Araromi kurmus a Ibadan

0

Wata gobara da tashi tsakar daren Asabar, ta kone kasuwar da ake sayar da kayan motoci da babura kurmus a Agodi-Gate, Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Ganau sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa gobarar wadda ta kone kasuwar Araromi kurmus, ta tashi ne bayan an maido wutar lantarki cikin dare.

“Gobarar ta tashi daga cikin daya daga kantinan cikin kasuwar bayan da aka maido wutar lantarki tsakar dare. Dama kuma kasuwar ta shafe watanni babu wutar lantarki. Bayan an maido da wutar ce tsakar dare, si gobarar ta tashi.” Haka wani mai suna Mumini Raji ya shaida wa PREMIUM TIMES.

Wakilin mu ya kuma gano cewa jami’an kashe gobara sun kasa kashe wutar da wuri, saboda motocin kashe gobarar ba su iya isa har inda aka yi gobarar.

“Jami’an kashe gobara sai da su ka rika jan bututun ruwan kashe gobara a kasa har zuwa kasuwar, saboda motocin su sun rasa ta inda zasu bi su shiga cikin kasuwar.”

PREMIUM TIMES ta tuntubi Shugaban Kashe Gobara na Jihar Oyo, Mashood Adewuyi, kuma ya tabbatar da faruwar mummunan lamarin.

“Gobarar ta tashi cikin dare, Allah ya rufa asiri ba ta ci rayukan mutane ko daya ba. Amma zuwa yanzu ba za mu iya bayyana yawan shagunan da su ka kone ba, saboda jami’an mu na ciki ba su gama tantancewa ba.”

Share.

game da Author