Jami’in hulda da jama’a na rundunar kashe gobara ta jihar Kano Saminu Abdullahi ya bayyana cewa gobara ta cinye mutum biyu ‘yan gida daya a jihar Kano.
Abdullahi ya fadi haka ne wa manema labarai ranar Asabar.
Ya ce an yi gobarar ne a wani gidan sama dake Zoo Road, dake hannun riga da da wurin hutawa na Kano Zoological Garden, a hanyar Sheka Municipal da misalin karfe 10:10 na daren Juma’a.
“Mutum hudu ne ke zama a gidan kuma gidan na da dakuna hudu, kitchen biyu, falo biyu da ban daki biyu wanda duk suka kama da wuta.
Abdullahi ya ce sun ceto mutum biyu da ran su amma mutum biyu sun riga mu gidan gaskiya.
“An ceto Fatima Salisu mai shekara 4 da mahaifinta Salisu Sani mai shekaru 45 amma kanwar uwargida Maryam Sani mai shekaru 19 da ita kanta uwargidan Nafisa Abdulkarim mai shekaru 28 sun mutu.
Ya ce rundunar ta ci gaba da gudanar da bincike domin gano abin da ya tada gobarar.
Idan ba a manta ba sakamakon binciken da hukumar kashe gobara ta fitar ya nuna cewa gobara ta yi sanadiyyar rayukan mutum 134 da dukiyar mutane da ya kai naira miliyan 635 daga watan Janairu zuwa Disambar 2020 a jihar Kano.
Hukumar ta ceto rayukan mutum 1,077 da kaya da ya kai Naira biliyan 2.56 a gobara 786 da aka yi a cikin shekarar 2020.
Rashin mai da hankali a lokacin da ake girki da rishon girki mai amfani da iskar gas da amfani da kayan wutan lantarki duk sune suka sa aka rika samun yawa-yawan gobara a jihar.
An kira lambar hukumar domin kawo dauki sau 693 amma kuma 184 daga ciki karya ne.
Hukumar ta yi kira ga iyaye da su daina bari kananan yara wasa kusa da rijiyoyi da wuraren dake da hadari.