Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (FAO), ta bayyana cewa an shafe tsawon watanni 10 a jere, daga watan Yuni 2020 zuwa Maris, 2021 farashin kayan abinci na tsulla tsadar tseren tsere wa karfin aljihun talakawa a fadin duniya.
Cikin wani rahoto da aka fitar a ranar Alhami, ya nuna akasarin abincin da tantagaryar taakawa su ka fi ci, ya rika yin tsadar da ya ke kokarin fin karfin talakawan.
Alkaluman kididdigar tashin farashin kayan abinci ya karu da kashi 2.1 cikin watan Maris, fiye da yadda ya ke a cikin watan Fabrairu.
Wannan karin hauhawar farashin kayanabinci kuwa, ba a taba ganin irin ta ba, tun bayan wadda aka gni cikin watan Yni, 2014
Rabon da man girki yay i tsadar da yay i cikin watan Maris, tun a shekarar 2011, kamar yadda sakamakon binciken da FAO ta fitar a farkon watan Afrilu din nan.
Sauran kayan abincin da FAO ta lissafa sun yi gwaron tashin farashi, sun hada har da madara da man buta, saralak,
Haka kuma farashin dawa ya fadi kasa warwas, sai kuma nama da kaji da
Shi ma naman kaji da farashin sukari, sai hauhawa su key i, har ta kai masu shan koko a wasu kasashe na tunanin shan sa lami salam, ba tare da zuba zukari ba.
Sai dai kuma wasu kasashen ana samun saukin farashin sukari, saboda yadda kasar Indiya ta rika dumbuza sukari zuwa kasashen duniya, domin sayarwa.
Daya daga cikin abinda ke dagula hankulan kasashe da dama shi ne tashin gwauron zabein farashin alkama, wadda da it ace ake sarrafa abinci da daman a manya da na jarirai.
Ana sa ran a duniya za a noma alkama mai tarin yawan tan milyan 785 a cikin shekarar 2021.
MALEJIN TSADAR RAYUWA A NAJERIYA:
Yayin da wasu kasashe ke ta kokarin ganin an kauce wa matsalar tsadar rayuwa, cikin watan da ya gabata ne dai PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda Bankin CBN ya rasa lakanin hana tsadar rayuwa ci gaba da yi wa talakawa kirbin-sakwarar-Ladidi.
A wancan labarin, an buga yadda taron da Kwamitin Tsare-tsare na Babban Bankin Najeriya CBN ya shirya domin labubo hanyoyin hana tsadar rayuwa tilasta wa tattalin arziki yin tsayuwar-gwamin-jaki, ya tashi ba tare da samar da wani lakanin da zai hana tsarar ta rayuwa ci gaba da yi wa talaka kirbin-sakwarar-Ladidi ba.
Masana sun yi tunanin cewa a taron manema labarai da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya kira yau Talata da rana zai shaida wa manema labarai cewa CBN zai kara kudin ruwan da bankuna da cibiyoyin hada-hada ke bai wa masu karbar ramce, lamuni da basussuuka.
To sai dai kuma a taron, Emefiele ya shaida masu cewa har yanzu adadin kudin ruwan da aka dora wa masu karbar lamuni daga bankuna na nan a kashi 11.5% bisa 100%, kamar yadda ya ke a cikin watan Fabrairu da Maris, ba a kara ba.
CBN ya nuna cewa wannan matsayi da su ka tsaya a kai, shi bankin ke ganin cewa zai iya samun karfin tura jaki ruwa, ta yadda tsadar rayuwar da aka shiga tsawon shekaru uku a jere za ta samu daidaito da farashin kayan abinci da na masarufi da kuma tattalin arziki.
Sai dai kuma a wurin taron Kwamitin, wasu sun so a dan kara adadin yawan kasafin kudin ruwan da ake dora wa masu karbar ramce a bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudade.
Shi dai kara kudin ruwa a kan masu karbar lamuni, ya na rage hada-hadar kudade a cikin tattalin arziki, kuma hakan dabara ce ta dakile tsadar kayan masarufi, kayan abinci da sauran kayayyaki.
Amma kuma yin hakan zai iya kara sa tattalin arzikin ci gaba da yin tafiyar hawainiya, ganin cewa kasar ba ta dade daga fita daga matsin tattalin arziki ba, wato ‘economin recession’ a Turance.
Sannan kuma dan karin kudin ruwan da za a yi din zai sa masu hada-hadar kasuwanci kasa sakin jiki su ramci kudade masu yawan da za su yi hada-hadar kasuwancin su.
‘Halin Damuwar Da Ake Ciki’:
Tattalin arzikin Najeriya ya fada halin kaka-ni-ka-yi, inda ba ya gaba sai dai baya, ga dimbin bashi ya cika ruwan cikin gwamnatin kasar, ga rashin aikin yi da ke karuwa, ga tsadar kayan abinci, ga kuma karancin samun kudin shiga ga dimbin jama’a. Sannan kuma kudin ba su da albarka kamar da.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda malejin tsadar rayuwa ke kara hauhawa a Najeriya, inda kayan abinci ya yi tsadar da shekaru 13 baya ba su gigita ’yan Najeiya irin haka ba.
Sannan kuma Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa (NBS), ta bada raboton karin tashin farashin kayan abinci cikin watan Fabrairu 2021, zuwa kashi 21.79, tashi mafi tsanani cikin shekaru 10 da suka gabata.
Farashin kayan abinci ya yi tashin-gwauron-zabo ne cikin watan Fabrairu biyo bayan hana safarar abinci da dabbobi da aka yi daga Arewa zuwa kudancin kasar nan.
Wannan tashin farashin kayan abinci kuwa ya wujijjiga marasa karfi sosai. Masu karfi kuwa sun rika saka makudan kudade sun a sayen abu kadan, ko kuma su sayi abin da suke saye da kudi kadan a baya.
Haka kuma a cikin watan Maris din nan, Hukumar NBS wadda hukumar gwamnatin tarayya ce, ta tabbatar da cewa malejin rashin aikin yi a kasar nan ya kai kashi 33.3 bisa 100, inda hakan ke nufin mutum milyan 23.2 a cikin majiya karfin ’yan Najeriya duk bas u da tudun dafawa wajen aikin yi.
Wannan matsalar rashin aikin yi kamar yadda NBS ta bayyana, shekaru 13 baya rabon da a fusknaci irin ta.
PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Bankin CBN ya gigice neman mafita, ganin yadda tattalin arzikin Najeriya ya yi tsayuwar-gwamin-jaki.
Yayin da tattalin arzikin Najeriya ke ci gaba da tafiyar-hawainiya da tafiyar-kura, a cikin yanayin karin yawaitar rashin aiki da tsadar rayuwa, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya dukufa wajen laluben mafita, ta hanyar yi wa wasu tsare-tsaren hada-hadar kudade garambawul a kasa.