A ranar Alhamis ne wasu jiga-jigan Kano da ya hada da hakshakin attajiri, Aminu Dantata da gwamnan Kano Abdullahi Ganduje suka sasanta Aliko Dangote da Abdussamad Rabiu, shugaban rukunin Kamfanonin BUA a Abuja.
A wajen taron sulhu wanda aka yi a gidan jihar Kano a Abuja ya samu halartar giwayen biyu da kuma wakilan masarautar Kano da manyan malaman Kano.
An tattauna matsalolin da ya shiga tsakanin artajiran biyu da kuma zargin da ake yi wai Dangote yayi babakere ne a kasuwar sikari don ya azazzalawa yan Najeriya su rika siyan sikarin da tsada.
Gaba dayan su sun musanta haka inda suka warware duk wani sabani dake tsakanin su sannan suka amince da su yi aiki tare domin ci gaban kasa baki daya.
Karanta labaran mu na baya:
RIKICIN GIWAYE BIYU: Yadda sukari ya hada Dangote da Abdul Samad Rabi’u ci wa juna kwala a kasuwa
A can baya cikin 2017 siminti ya taba hada Aliko Dangote da Abdul Samad Rabiu dambe a tsakiyar kasuwar Najeriya. A wannan karo kuma, wani sabon rikicin ne ya taso tsakanin abokan biyu, kuma ‘yan gari daya, wato Kano.
Dangote, wanda ya fi kowa karfin arziki a Afrika kakaf, kuma na shida wajen karfin arziki a duniya, ya sake tada wani rikici tsakanin sa da Abdul Samad Rabi’u, shi ma wani kasaitaccen attajirin a Najeriya, kuma abokin sa.
Kamar wancan, wannan rikicin, shi kuma wannan ya danganci kokawar hakkin mallakar wani filin yin sukari ne a Jihar Ribas.
Acikin watakwafen wasika da Dangote ya rubuta wa Ministan Ciniki da Masana’antu, Niyi Adebayo, kuma PPREMIUM TIMES ta ga kwafen wasikar, Aliko Dangote a matsayin sa na Shugaban Dangote Sugar Refinery Plc, ya bayyana cewa kafa masana’antar yin sukari da kamfanin BUA, mallakar Abdul Samad Rabiu ya yi a Fatakwal ya kauce wa ka’idojin dokokin fitar da kaya kasashen waje.
“Nazarin da Hukumar Sukari ta Kasa ta (NSDC) gudanar ya nuna karara cewa kamfani BUA ya kasa zuba gagarimin jarin da ya kamata ya zuba a cikin gida Najeriya, kuma ya ki bin yarjejeniyar da ya sa wa hannu.”
Haka wasikar da Dangote ya aika wa Minsita Adebayo takunsa, waddayasawahannu shi da John Coumantaros, Shugaban kamfanin filowa na Flour Mills of Nigeria Plc.
“Yayin da BUA ke ikirarin cewa ya na zuba jarin aikin sukari domin a rika daga masa kafa wajen shigo da kaya daga waje, to a gaskiya tantagaryar sukarin ne ya ke shigowa da shi daga waje.”
Wannan tankiya ta kunno kai cikin watan Yuni, 2020 yayin da kamfanin simintin BUA, wanda mafi yawa na Abdul Samad ne, ya samu izni a bude masa wuraren aiki uku a Obu Okpella, Jihar Edo.
BUA ya zargi kamfanin Dangote Cement da haddasa kulle masa wuraren da ‘yan sanda su ka yi.
Yayin da su Dangote ke nuna rashin yarda a kafa masana’antar sukarin, bisa hujjar cewa an karya ka’ida, shi kuma Rabiu ne ikirarin cewa Shugaba Nuhammadu Buhari ne ya bada iznin ya kafa masana’antar.
Shi dai BUA ya rattaba yarjejeniya da wani kamfani na kasar Faransa, mai suna Axens cikin Satumba, 2020 domin su yi hadin guiwar kafa katafaren masana’antar tace danyen mai ganga 200,000 a kullum ta sinadarin kemical a Akwa Ibom.
Shi kuma Dangote ta sa da ke Lagos za ta rika tace danyen mai ganga 650,000 a duk rana daya, a Lagos.
Arzikin Dangote ya kai dala bilyan 12.4, shi kuma Abdul Samad wanda shi ne na uku a karfin arziki a Najeriya, na sa arzikin ya kai dala miliyan 5.5, kamar yadda mujallar Forbes ta dora su a kan sikeli.
Tsohuwar Rigimar Dangote Da AbdulSamad Rabiu:
Cikin watan Disamba, 2017 PREMIUM TIMES HAUSA ta buga rahoton yadda rikicin ma’adinainya harde tsakanin Dangote da BUA, har su ka garzaya kotu.
A cikinlabarin an ji yadda Kamfanin Dangote Group ya zargi BUA Group da aikin hakar ma’adinai a kadadar ma’adunai mai albarka, mai lamba No. 2541, da ke kan iyakar Oguda da Ubo, a yankin Okene, cikin jihar Kogi.
Wannan fangamemen wurin hakar ma’adinai dai ya haddasa rikici tsakanin manyan kamfanonin biyu da kuma Gidan Sarautar Omadivi na Okene, jihar Kogi.
Dukkan kamfanonin biyu dai su na ikirari har a gaban kotu da kuma wasikar da aka tura wa Shugaba Muhammadu Buhari korafi, cewa su ne aka bai wa lasisin hakar ma’adinai a wurin.
Ma’aikatar Ma’adinai da Karafa ta Tarayya ita ce ke da alhakin bayar da iznin amincewa kamfani ya haki ma’adinai a ko’ina cikin kasar nan.
Sakamakon kukan da BUA ya tura ofishin Shugaban Kasa, a ranar 4 Ga Disamba, 2017, Dangote Group ya amince a warware rikicin a bisa ka’idar da dokar kasa ta shimfida a cikin kundin dokokin kasar nan.
HUJJOJIN KAMFANIN BUA
Shi dai Shugaban Kamfanin BUA, Abduksamad Isyaka Rabi’u, ya rubuta wa Shugaba Buhari wasika a ranar 4 Ga Disamba, dangane da kiki-kakar da ke tsakanin Kamfanin sa da na Dangote.
Korafin wanda jaridu da dama sun buga shi, ya zargi Ministan Ma’adinai da yi wa BUA kafar-ungulu ta hanyar mara wa Dangote Group baya a kan rikicin.
Ya zargi Minista Kayode Fayemi da yin karfa-karfar kwace masa lasisin hakar ma’adinai mai lamba 18912 da kuma 18913 wanda su ke hakar ma’adinai a Obu-Okpella cikin Karamar Hukumar Etsako da ke jihar Edo.
Rabi’u ya jajirce cewa Kamfanin sa ne ke da hakkin hakar ma’adinai a wurin, domin a cewar sa, tun a ranar 17 Ga Yuni, 1998 aka ba shi lasisi.
HUJJOJIN KAMFANIN DANGOTE
Kamfanin Dangote ya ce ya sayi lasisin hakar ma’adinai a wurin daga hannun AICO Ado Ibrahim Company Limited a cikin 2014.
Dangote ya ce hujjoji da dama sun tabbatar da cewa Ma’aikatar Ma’adinai ta Tarayya ce ta bai wa AICO lasisin wanda Dangote ya saya a hannun kamfanin.
Dangote ya kawo hujjoji masu dauke da lambobin lasisi da dama.
Yayin da Hukumar Kula da Ma’adinai ta Kasa ta tabbatar da bai wa AICO lasisin hakar ma’adinai, kamar yadda Dangote ya tabbar, shi kuma gidan sarautar Atta Omadivi sun zargi Ma’aikatar Kula da Ma’adinai ta kasa da nuna bangaranci su na goyon bayan Dangote.
Duk da cewa dai rigimar na kotu, a gefe daya kuma an gabatar da korafin nuna son kai ga BUA Company.