Gwamnan jihar Abubakar Bello ya bayyana cewa Boko Haram ta mamaye kananan hukumomin Kaure da Shiroro dake jihar. Ba mamaye garuruwan ba kawai, sun kwace wa magidanta matayen su sun rabawa kan su sannan sun kafa tuta a tsakiyar Garuruwan.
A sanarwar da babban mai ba gwamna Bello shawara kan watsa labarai Mu’awuya Muye ne ya sanar da wadannan kalami na gwamna a shafin sa ta tiwiti.
“Boko Haram sun kwace yankin sun kuma kafa tutarsu, ina tabbatar da hakan a yanzu”
Gwamna Bello ya ce ya dade ya na kwankwasa kofar fadar gwamnati a Abuja domin ya kai kukar sa kan kwararowar Boko Haram jihar a gaggauta daukar mataki akai amma ba ayi komai ba a kai.
” Wannan shine na ke ta jeka ka dawo, kullum in Abuja domin in nuna wa gwamnati hatsarin dake tattari da kwararowar boko Haram jihar da halin da mu ke ciki domin a dau mataki tun da wuri kafin ya kai haka. Yanzu abin tsoron shine Ita kanta Abuja bata tsira ba.
Sambisa na da nisa daga Abuja, amma Kaure kusa ta ke da Abuja, saboda haka a halin yanzu babu wanda ya ya kubuta daga kwararowar su Abuja ita kanta.
” Ni fa yanzu na gama sauraren wani kan tsaron jihata, abin ya kai ni makura zan dauki mataki kai tsaye yanzu.
Discussion about this post