Shugaban hukumar kula da makarantun Al’qur’ani da Islamiyyu na Jihar Kano, Gwani Yahuza-Danzarga yayi waiwaye akan tarihin yadda aka fara kirkiro makarantun Allo, wato tsangaya a musulunci da kuma lalacewarsa a kasar Hausa.
Malam Yahuza-Danzarga a hira dayayi da jaridar PREMIUM TIMES HAUSA a ranar Laraba, yace a zamanin khalifa Sayyidina Umar Dan Khattab aka fara kirkiro makarantun tsangayu domin a koyawa yara karatun Al’qur’ani.
“Wata rana sayyidina Umar ya fito yana rangadi sai ya ga yara suna gararamba a gari ba’a kulawa dasu, sai yayi tambaya me ya faru akabar yara haka, sai aka gayamasa cewar iyayensu maza suna wajen yaki anbar yaran ne tare da iyayensu mata a gida.
“Sai Sayyidina Umar yace bai kamata a barsu haka ba sai yayi umarni a tattarasu a dauko malami ya dinka koya musu karatun Al’qur’ani kuma duk wanda ya kasa sai a rubuta masa a Allo kuma a ringa biyan malamin albashi daga bitalmanin gwamatin musulunci, inji Yahuza-Danzarga
“Bayan haka, Sayyidina Umar yana zagawa yana ganin yadda ake karatun Allon yana jin dadi, sai ya kuma yin umarni da cewa a cigaba da bude makarantun allon a kewayen garin Madina kuma malaman a ringa biyansu daga bitalmani.
“Wata rana sai Sayyidina Umar yayi tafiya zuwa bude kasar Sham (Syria) yayi kusan wata daya acan mutane suna son ganinsa, a lokacin da aka samu labarin zai dawo sai a debi dalaban makarantun Allon aka je aka tare shi a ranar Alhamis har zuwa ranar Juma’a ana murnar dawonsa.
“A ranar Alhamis da Juma’a makarantun Allon ba’ayi karatu ba sai aka mayar dasu ranekun hotu wadda shi ne haryanzu ake yin hotun Alhamis da Juma’a a makarantun Allo dana Islamiyyu a kasar Hausa.
“Anan Najeriya, a kasar Borno, Shehun Borno Mai-Ummi Jalmi shi ya fara kafa makarantar Allo da ake kira da maharam (wajen koyan karatu) inda yara suke zuwa suyi karatu su koma gida, sarki Jalmi shi yake daukar nauyin malaman masu karantarwa.
“A Kano kuma, Sarki Ali Yaji, wanda yayi mulki daga 1349 zuwa 1385 shi ne Sarki na goma sha daya a jerin sarakunan Kano, shi ya fara kafa makarantar Allo a Kano.
“Sarkin Kano Muhammadu Rumfa wanda yayi mulki daga shekarar 1463 zuwa 1499 shi ne Sarki na ishirin a jerin sarakunan Kano, shi ma ya bunkasa makarantun Allo inda ya kafa wata cibiya da ake kira Albir wanda yara suke zuwa suna karatun suna komawa gida.
“Dukkannisu sarakunan Borno dana Kano su suke daukar nauyin malaman makarantun Allon.
“A baya, shehu Usman Danfodio shi ya fara gina makarantar Allo ta kwana kuma da malamai da dalibai duk shi yake daukar nauyinsu.
“Haka tsarin yake har zuwan turawan mulkin mallaka, harkar ta lalace mulki ya bar hannun sarakuna, aka raba masautu da iko, sai kuma malamai da iyayan yara aka bar masu harkar makarantun Allo wadda a karshe bara ta shigo domin aci abinci.
“A musulunci babu bara a makarantun Allo na tsangaya, abinda daya kawo bara shi ne janyewar gwamnati (Sarakuna) daga harkar gudanar da makarantun Allon wadda shi ne ya jawo lalacewarsa a kasar Hausa.
“Yanzu a Kano, gwamnatin Abdullahi Ganduje ta samar da hukuma wanda take lura da harkar makarantun Allon makamanciyar irin wacce sarakunan Kano da Borno, da kuma Sarkin Musulmi Shehu Usman Danfodio suka yi a baya domin dawo da daraja da kuma inganta karatun Al’qur’ani a Kano.
“Majalissar dokokin Jihar Kano a shekarar 2015 tayi dokar data samar da hukumar kula da harkokin Tsangayu da Islamiyyu ta Jiha domin kawo gyara a harkar makarantun Al’qur’ani wadda shi ne kanawa suka gada.
“A yanzu gwannatin jihar Kano tanada makarantun Tsangayu na zamani guda goma sha biyu wadda ake biyan malamai kuma ana ciyar da dalabai daga asusun gwamnatin Jiha.
“Tsangayun guda goma na kwana ne guda biyu koma jika ka dawo, kuma nan bada dadewa ba za’a bude wasu sabobbi a jihar, ahankali mutane zasu fahimci manufar gwamnati na cigaban al’ummarta, inji Gwani Yahuza-Danzarga.
Discussion about this post