Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa ‘yan bindiga tofin tir, bisa dalilin kashe dalibai uku na Jami’ar Greenfield University daga cikin wadanda su ka yi garkuwa da su a Kaduna.
Buhari ya kuma umarci a tura hatsabiban jami’an tsaron da za su gasa wa wadannan mahara azaba, bayan sun ceto sauran daliban da ke hannun su.
Kwamishinan Harkokin Tsaro na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne a ranar Talata ya sanar cewa an tsinci gawareakin dalibai uku daga cikin daliban jami’ar da aka yi garkuwa da su.
Kakakin Yada Labarai na Shugaba Buhari, Garba Shehu ya fitar da sanarwar tir din da Shugaba Buhari ya yi wa ‘yan bindiga a ranar Asabar.
Ya ce ya nuna takaicin yadda ‘yan bindiga su ka katse wa daliban kyakkyawar rayuwar su da su ka faro kan turbar gina kan su da kuma gina kasa.
“Ina mai matukar taya iyayen su da sauran ‘yan uwan su ta’aziyya da jimamin rashin daliban su uku. Allah ya gafarta masu.”
Buhari ya mika ta’aziyyar Gwamnatin Tarayya ga iyaye da dangin wadanda aka kashe, kuma da Gwamnatin Jihar Kaduna.
Jami’ar Greenfield Universiy inda aka sace daliban dai a daji ta ke, kan hanyar Abuja daga Kaduna.
Har yanzu ‘yan bindiga na rike da sauran daliban, yayin da gwamnan Kaduna El-Rufai ya yi tsayuwar-gwamin-jaki, ya ce ko dan sa aka yi garkuwa da shi, ba zai biya kudi a sako shi ba.
Discussion about this post