Duk da ba dan jihar Kaduna bane, shugaban masu rinjaye na majalisar tarayya, Honarabul Ado Doguwa ya roki majalisar tarayya ta cikawa marigayi Sarkin Lere Abubakar, da dan majalisa mai wakiltar Lere a majalisar Tarayya, Honarabul Suleiman Aliyu Lere, na su saka baki a gyara wutan karamar hukumar Lere da ake fama da rashin sa.
Idan ba a manta ba, tun bayan rantsar da shi a watan Faburairu, abu na farko da Honarabul Lere ya fara yi shine mika kudiri don majalisa ta kwankwasa wa hukumar samar da wutar lantarki ta kasa ta waiwayi karamar hukumar don kawo karshen matsalar wuta da ya dauki watanni ana fama da shi.
” Wannan shine babban burin marigari Sarkin Lere Abubakar, da dan majalisa marigayi Suleiman Lere. Da na je ta’aziyyar marigayin a garin Lere, na gana da sarkin Lere marigayi Abubakar, a lokacin rokon da yayi min shine don Allah in taya shi mika sakon nan ga ‘yan majalisa da Kakakin majalisa, Femi Gbajabiamila, cewa marigayi Suleiman Lere ya mika wannan kuka na mutanen Lere, shima yana rokon mu duka mu sa baki wannan buri na sa ya cika. Kwana daya bayan na baro Lere sai sai aka kira ni kuma cewa, Sarki Abubakar ya rasu shima.
Hon Doguwa ya roki majalisar ta yi kokarin ganin ta cika wa dan majalisar da sarki burin su.
Idan ba a manta ba a kwanaki hudu bayan rasuwar dan majalisar dake wakiltar Lere a majalisar tarayya, Honarabul Suleiman Aliyu, ya rasu sarkin Lere Abubakar II shima ya rasu.
Allah ya gafarta musu, Amin.