WUTA SALLAU’: Yadda cin lafiyayyar shinkafa dafa-duka ya gagari mai karamin karfi a Najeriya -NBS

0

Farashin sinadaran kayan dafuwar shinkafa dafa-duka ya karu sosai tsawon shekara daya, daga Maris 2020 zuwa Maris 2021, ta kai dafa lafiyayyar shinkafa dafa-duka, wato ‘jollof rice.’’

Wannan farashi dai ya karu a daidai kuma lokacin da shinkafa da wake da mai da yaji wato garau-garau ya ke neman gagarar talaka sakamakon tsadar da waken kan sa ya tsula, baya ga tsadar shinkafar ita ma.

Cibiyar Binciken Kwakwaf ta SBM ce ta fitar da wannan kididdiga cewa farashin yadda ake hada lafiyayyar shinkafa dafa-duka ya karu da tsadar da har ta kai shi tashi daga 7.8 zuwa 18.17 daga Maris 2020 zuwa Maris 2021, cikin shekara daya.

Binciken Kwakwaf din da SBM ya fitar akan dan karen tsadar da shinkafa dafa-duka ta yi, an bi kasuwanni har 13 domin tantance farashin kayan miya da kayan kamshin miya a dukkan sassan kasar nan,

Hukumar Kididdigar Alkaluman Bayanai ta Kasa, NBS, wadda hukuma ce ta gwamnatin tarayya, ta fitar da kididdigar bayanan tsadar hada abinci lafiyayye kamar shinkafa dafa-duka, cewa ya tashi har zuwa kashi 18.17.

Kayan Hadin Shinkafa Dafa-duka: Talaka Sai Gani Sai Hange:

A yayin da da dimbin jama’a su ka koma cin shinkafar gida, kuma garau-garau ba tare da miya ko nama ba, NBS ta bayyana yadda kayan hadin dafa-duka.

Kafin talaka ya hada lafiyayyar shinkafa dafa-duka (jallof rice), sai ya tanadi kudin da zai sayo sinadaran kamshin da zakin abinci da su ka hada da ‘curry’, ‘thyme’, dunkulen knorr, man kuli, ko man ‘turkey’, nama, barkona, tattasai da attaruhu, tumatir, gishiri da kuma albasa.

Rahoton ya ce idan magidanci zai so a dafa masa lafiyayyar shinkafa dafa-duka da za a ci a gidan a koshi, sai ya kashe naira 7,400, wato sai ya kashe kashi 25 bisa 100 na mafi kannatar a albashin ma’aikatan Najeriya.

“Wannan makudan kudaden da talaka zai nemo ya kashe idan gidan za za a ci lafiyayyen abinci, farashin ya zo da mamaki, domin dube kan iyakokin Najeriya da aka yi domin samun saukin farashin kayan abinci.

“Dalilai da dama ne su ka haifar da wannan tsadar rayuwa ta tsadar kayan abinci.

“Sai kuma rufe kan iyakokin Najeriya, tsawon shekara daya dimin saukin kuncin yaruwa, hakan bai samu ba, dai dai dan karan tsada da kayan abinci su ka yi.

Rahoton dai ya nuna shinkafa dafa-duka ce abinci da aka fi kashe wa kudi kafin a dafa a zuba cikin kwano a ci.

Share.

game da Author