“Wasu shaidanu” na shirya bidiyon bogi don bata min suna – Pantami

0

Ministan Harkokin Sadarwa Isa Pantami ya yi korafin cewa “wasu shaidanu” na kulle-kullen fito da sani shiryayyen bidiyon bogi a kan sa, don kawai su bata masa suna.

Kakakin Yada Labarai ta Minista Pantami, mai suna Uwa Sulaiman ce ta fitar da wannan sanarwa, ranar Talata a Abuja.

Yayin da aka taso Pantami gaba kan wasu kalamai ko furucin da ya rika yi a shekarun baya, Ministan ya fito ya nesanta kan sa da kalaman, tare da nuna cewa daga baya ya gano akwai kuskuren fahimta da yarinta a lokacin.

Ita ma Gwamnatin Najeriya ta fito ta goyi bayan Pantami, kuma ta ragargaji masu kokarin yi masa bi-ta-da-kulli.

Sanarwa Daga Minista Pantami:

Shaidanu Na Neman Hadin Kan Lalatattun Da Za Su Shirya Bidiyon Bogi Domin Bata Min Suna:

“Mun samu sahihin rahoton sirri mai nuna cewa shaidanun da ake biya makudan kudade su na ruruta mummunan kamfen a kan Ministan Sadarwa Isa Ali Ibrahim Pantami, yanzu kuma sun kamo hanyar matakin shirya tuggu da sharrin shaidancin su na gaba.

“A wannan mataki, wadannan shaidanu sun shiga fagamniyar neman lalatartun da za su hada kai da guiwa domin su shirya kuma su fito da tsararrenPantami na bogi, wanda da zai nuna kamar Minista Pantami na da hannu tsamo-tsamo a cikin wani mugun shiri, don kawai su bata masa suna.

“Ba mu yi mamakin wannan mummunar aniya ta su ba, musamman ganin cewa irin matsin-lambar sharri da yarfen da su ka kure maleji su na yi wa Mai Girma Minista, bai yi wani tasirin munana shi ko muzanta shi ba.

“Bayan wadannan shaidanu sun kirkiri karairayi da sharrin danganta Minista da ta’addanci, duk kuwa da matsayin da ya rika dauka inda ya rika barranta da ta’addanci da ‘yan ta’adda, ciki har da Boko Haram, wadannan shaidanu yanzu sun kai ga kokarin kirkiro takardun bogi, wadanda munin su ya kai su kawo barazana ga zaman lafiya a kasar nan.

“Sai dai kuma abin godiya shi ne ‘yan Najeriya masu son zaman lafiya ba su bayar da kai borin shaidanu ya hau kan su ba. Domin kuwa sun gane sharri ne kuma batunci ne.

“Saboda haka wannan sanarwa, wata zaburaswa ce ga daukacin jama’a domin su san sharrin da wasu shaidanu ke kokarin kitsawa. Kuma sanarwar gargadi ce ga duk wani mai tunanin za a hada kai da shi domin a kulla wannan sharrin cewa akwai hukunci ga duk wanda ke da hannu a ciki.

“Mai Girma Minista ba fa zai zauna ya zura ido wasu shaidanu da batagari su zubar masa da kima da mutunci a matsayin sa na jagoran al’umma ba. Kuma a matsayin sa na Masanin Addinin Musulunci, sannan ma’aikacin gwamnati, ba zai tsaya ya zura ido wasu ‘yan kakudubar da ake biya makudan kudade a boye da babu son gaskiya ko tsoron Allah a zukatan su, su bata masa suna ba.

Share.

game da Author