Tsohon Shugaban APC na Jihar Kwara, Iyiola Oyedepo, ya bayyana cewa littafin sa mai suna “Karairayi 21 Da ‘Yan Siyasa Ke Shirga Wa Talakawa Lokacin Kamfen”, ya rubuta su ne domin fallasa dabarun da ‘yan siyasa ke yi idan su na neman kuri’u dga hannun jama’a.
Oyedepo ya yi wannan furucin a Ilorin babban birnin Jihar Kwara, a lokacin da ya ke gabatar da littafin ga jama’a.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa littafinn mai shafuka 140, ya kushi babi 21 na karairayi 21 da ‘yan siyasa ke yi domin ribbatar talakawa su jefa masu kuri’a.
Marubucin littafin ya bayyana cewa ya rubuta littafin ne domin ya ilmantar da talakawa sanin wanda ya kamata su zaba tun yayin kamfen, domin idan su ka yi kuskuren zaben-tumun-dare, to za su ci gaba da zaman yin da-na-sani da cizon yatsa na tsawon shekaru hudu.
“Wato na zauna ne na yi nazarin irin kalamai da alkawurran da ‘yan siyasa mu ke yi domin cin zabe. Wasu batutuwan akwai su, amma ana murguda zance ko a canja ma’ana ko manufa da gangan a wurin kamfen don kawai a ci zabe kuma a karkatar da hankulan jama’a. A karshe sai ka ga wadanda jama’a su ka dora kan mulki, ba su biya masu bukatun da su ka wajaba su biya masu ba.
“Ni littafi na ya karkata ne wajen wayar wa talakawa ‘yan Najeriya kai, bai karkata wajen goyon bayan ‘yan siyasa ba.
“Su fa ‘yan siyasa ‘yan yaudara ne. Dole sai sun yi yaudarar nan. Kamar mai neman aiki ne, wanda zai rubuta har abin da ba gaskiya ba ne dangane da shi, don dai kawai ya samu aiki, bukatar sa ta biya idan ya samu aikin.
“To ya rage ga masu zabe su sani cewa daga yanzu ba za mu sake aminta ko lamuntar mayaudara ba. Yaudarar ta yi yawa haka nan. Daga wannan zabe zuwa wannan sai kyankyashe gurbatacciyar gwamnati ake ta yi duk bayan shekaru hudu.”
Ya ce ya na bukatar kungiyoyin wayar da kan jama’a su yi amfani da littafin sa wajen wayar wa jama’a kai su daina zaben mayaudara.
Daga cikin wasu lakanoni da ‘yan siyasa ke amani da su su ka yaudarar jama’a da karairayi, akwai: Yawan jama’a, addinanci, kudi, siyasar ubangida, kabilanci, bangaranci, rikicin kabilanci da fadace-fadacen makwautan kabilu, kakaba wanda jama’a ba u so kan takara, dukiya, shahara, talaucin masu zabe da rashin gane inda aka dosa ga masu zabe sai kuma amfani da tsarin federaliyya.
Akwai kuma bambancin dan Kudu ko dan Arewa, kakaba tsarin karba-karba, dora matasa kan turbar dabanci da jagaliyanci, bijiro da ayyukan taimakon jama’a ga talakawa don a ja hankalin su su zabi mai yi masu taimakon daga baya, amfani da fifikon ilmi, ko fifikon dukiya, bambancin attajiri da fakiri, siyasar gado ko nuna fifikon asali na sarautar gargajiya.
Manyan ‘yan siyasa da dama na jihar Kwara sun halarci taron kaddamar da littafin, wasu kuma sun tura wakilan su.