TUBALIN GININ KISHIN TALAKAWA: Shekaru 38 Bayan Rasuwar Aminu Kano, Daga Mansur Ahmed

0

“A takardar barin aikin Malam Aminu Kano da ya rubuta ranar 4 Ga Nuwamba, 1950, ya ce “na hango wani haske a can nesa tsakanin sama da ƙasa. Don haka zan yi kokari in riske shi, ko da a ce ni kadai ne ko ni da wani.”

Adalcin Malam Aminu Kano bai tsaya ga mutane ba kawai, har ga tsuntsaye da dabbobi, shi ya sa duk lokacin da ya yi jawabi ya na cewa jama’a ku yi wa dabbobi da tsuntsaye adalci domin akwai hakkin su a wuyan mu. Misali wata rana Malam Aminu Kano ya shiga cikin birnin Kano domin gabatar da ta’aziyya sai ya hangi wani ɗan kwuikwiyo a kwance tsananin yunwa ta sa ko tashi ba ya iya yi. Sai yara ne su ke ta jagwalgwala shi, sai Malam ya tsaya ya bayar da kudi ya ce a sayo wa karen nan abinci.

Hikayar Aminu Kano Da Kare:

Bayan ya dawo gida tunanin karen nan ya dame shi sai ya ce to gobe kuma waye zai ba shi abinci? Dan haka ya sa aka je aka daukko masa karen nan ya kawo shi gidan sa har ya saka masa suna Jaura saboda lokacin ana cikin hunturun sanyi ne.

An haifi marigayi Malam Aminu a shekarar 1920 a cikin birnin Kano, a Unguwar Sudawa, ya fito daga zuriyar Fulanin Gyanawa mahaifin sa malami ne kuma alkali.

Da farko ya so ya zama lauya, amma saboda sanin halin sa sai maganar ta girgiza (Resdan) na Kano na waccan lokacin, domin kowa ya san halin Malam Aminu Kano na yaƙi da akidun Turawa na danniya da zalunci tun ya na ɗan makaranta a “Middle.” Don haka in ya samu dama ya zama lauya, to zai fitini Turawa a kan baƙin mulkin mallaka. Saboda haka sai aka dakile maganar ba ta je ko’ina ba.

Na biyu; sai ya ce ya na so ya zama likita nan ma aka ce babu isassun yaran da za’a haɗa su, su je Legas makaranatar koyan aikin likita da ke Yaba.

Na uku sai ya ce ya na so ya yi aikin dan sanda. Nan ma sai aka ce masa tsawon sa bai kai ba da Inci ɗaya.

Na huɗu, sai ya ce to ya na so ya zama malamin asibiti. Nan ma aka ce a’a sai dai ya yi aikin koyarwa a makaranta. Shi kuma bai cika son koyarwa ba.

Wasu daga cikin mutane sun yi ta yayatawa tare da tunanin akwai rashin jituwa mai karfi tsakanin Malam Aminu da Sardaunan Sakkwato Ahmadu Bello da Tafawa Balewa, wannan zance ba shi da tushe domin ko bayan rasuwar su an jiyo muryar Malam Aminu a laccoci daban daban ya na yabo da bayyana Sardauna a matsayin mutum mai amana, juriya, jajircewa kuma ya yi wa Arewa abin da ba za’a manta da shi ba.

Darussan Da Ke Kunshe Cikin Wasikar Da Aminu Kano Ya Aika Wa Sardauna, A 1958:

Ga kwafin wata Wasika da Aminu Kano ya aika wa Sardauna lokacin a ranar 8 Ga Afrilu, 1958.

39 Sudawa,

Akwatin Gidan Waya 744,
Kano.

8 Ga Afrilu 1958.

Zuwa Ga Alhaji Ahmadu Sardaunan Sakkwato,

“Ina mai farin ciki shaida maka cewa na sadu da wasikar ka a ranar 1 ga wannan wata. Hakika, shirye – shiryen ka da su ke cikin wannan takardar, babu shakka za su taimaki musulman kasar nan. Allah ya saka maka da mafificin alheri.

“Kuma zan yi amfani da wannan dama wajen bayyana maka farin ciki na game da irin karɓar da ka ke yi min, da kuma yadda ka nemi da in tuntube ka a kan duk wani batu da na ji zan iya yi a kan haka. Na tabbata wannan zai amfani abokantakar mu, wadda mu ka kulla tun lokacin da ba daya daga cikin mu da ya san zai rike wani muƙami a gwamnati.

“Na yi alƙawarin ziyartar ka a duk lokacin da na zo Kaduna komai kuwa irin yanayin ayyuka na.

“A cikin wasikar ka na ga ka kawo wani batu da ya dade a raina, wanda shi ne ‘yancin kai ga Arewacin Najeriya da ma kasa baki daya. Ka tuna da abin da na faɗa maka a cikin jirgin ruwa kan hanyar mu ta zuwa Landan na ce ko da yaushe zan goyi bayan ka a kan maganar yancin kai, ka kira ni a duk lokacin da ka bukace ni zan taimaka a duk wata hanya da zan iya. Amma ina fatan za ka yi nazari a kan shawararin da zan bayar sannan ka kula da wasu tsiraru da za su yi kokarin biyan bukatun kan su da sunan yancin kai.

“Ina fatan za ka sanar da ni a cikin lokaci duk lokacin da buƙatar hakan za ta taso saboda yanayin tafiye-tafiye na.

“Ina yi maka fatan kammala azumin watan Ramadan lafiya musamman a cikin wannan yanayi na zafi. Allah ya shirya mana wannan kasa kuma ya daukaka ta.”

Naka,

Aminu Kano.

Nasarorin Da Aminu Kano Ya Samu A Rayuwa:

Wadanne nasarori ya samu a gwagwarmayar sa? Allah ya kaddara masa haddar Al-qur’ani Mai Girma yadda duk inda zai gabatar da jawabi da wahala bai kawo aya ya fassara da take da alaka da taron ba.

Haka lallai Malam ya samu gagarumar nasara a gwagwarmayar sa na kawo karshen zalunci. Gwagwarmayar Malam ta tilasta wa sarakunan gargajiya su sake salon mulkin su tare da kawo karshen noma kyauta a gonakin masu mulki a kyauta. Ya kuma kawo karshen haraji da jangali. Sannan tsayuwar dakan da Malam ya yi ya bai wa ‘ya’yan talakawa damar samun ilimi zuwa kowanne mataki sannan da rike mukaman siyasa da gwamnati wanda a da ya takaita ne kawai ga gidajen mulki.

Yau a Najeriya tun daga kan shugaban ƙasa har kan wanda ya fi kowa kankantar mukami ‘ya’ƴan talakawa ne.

A yau a ko’ina a Arewacin Nijeriya mutane na kokarin sanin tare da kare hakkokin su da kundin tsarin mulkin kasa ya ba su. Su na kuma shiga cikin harkokin bunkasar dimokaradiyya domin cigaban kasar su. A yau akwai yancin faɗin ra’ayin ka da walwala wanda masu mulkin mulukiya su ka hana al’ummar su a wancan zamanin .

Wasu Da Cikin Manyan Abokan Gwagwarmayar Aminu Kano:

1. Malam Sa’adu Zungur

2. Bello Ijumu

3. Musa Kaula

4. Baballiya Manaja

5. Alhaji Adamu Danjaji

6. Magaji Dambatta

7. Mudi Sipikin

8. Malam Abba Mai kwaru

9. Malam Illah Ringim

10. Muhammad Danjani Hadejia

11. Malam Audu Angale

12. Alhaji Dauda Dangalan

13. Hajiya Asabe Reza

14. Hajiya Gambo Sawaba

15. Malam Lawal Dambazau

16. Mrs. Bola Ogunbon

17. Muhammadu Abubakar Rimi

18. Sule Lamido

19. Gambo Hawaja

20. Sabo Bakin Zuwo

Da sauran su da dama.

An saka sunan Malam Aminu Kano a, Filin Jirgin Saman Kasa da Kasa da ke Kano, Asibitin Koyarwa na Kano, Aminu Kano Collage of Islamic and Legal Studies, Filin Taro na Aminu Kano Triangle da ke Dutse, Jihar Jigawa. Sai Titin Aminu Kano Way a Kano, Jigawa, Lagos, Bauchi, Kaduna da Abuja da sauran abubuwa masu yawa.

Ya rasu ya bar mata daya, Aishatu. wadda Allah ya yi wa rasuwa ranar 22 Ga Mayu, 2017 da ‘yar sa ɗaya Maryam. Sannan ya bar gida daya da gona ɗaya. Allah ya jikan Malam da iyayen mu da dukkan al’ummar musulmi.

Mansur Ahmed ya rubuta daga:

Gidan Siyasar Sule Lamido, CON.

Ranar 17 Ga Afrilu, 2021.

Share.

game da Author