Hukumar EFCC ta tsare tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari ta nay i masa dogayen tamboayoyin da su ka jibinci zargin wawurar makudan kudaden da ake yi masa.
PREMIUM TIMES ta gano cewa Yari na can a tsare ofishin EFCC na Sokoto, har tsawon sa’o’i takwas ana yi masa tambayoyi a lokacin dake rubuta wannan labari.
PREMIUM TIMES a baya ta buga labarin yadda EFCC ta aika wa Yari da wasikar gayyata a ranar 6 Ga Afrilu, 2021, inda ta nemi ya kai kan sa ofishin EFCC na Sokoto a ranar 8 Ga Afrilu.
Sai dai kuma majiyar mu ta bayyana cewa Yari bai kai kan sa ofishin ba, har sai a ranar Talata, 20 Ga Afrilu, wato ya yi karin kwanaki 12 kenan.
“Yari ya kai kan sa ofishin EFCC na Sokoto, wajen karfe 11 na safiyar Talata.” Inji majiyar mu.
Har zuwa ssafiyar Laraba dai Yari na ofishin EFCC zuwa 7 na safiya.
“An bayar da belin sa, amma ya kasa cika sharuddan beli.”
EFCC ta dade ta na haska cocilar ta kan Yari, dangane da yadda ya “tsoma dungulmin hannun sa cikin kudaden Paris Club daga 2017.
Cikin wasu takardun bayanai da aka gabatar a EFCC, a cikin watan Janairu, 2017, an zargi Yari da “kumbiya-kumbiyar harkallar naira biliyan 19.439 daga kudaden Paris Club da gwamnatin tarayya ta maida wa jihohi 36.”
Dama kuma EFCC ta nemi kotu ta ba ta ikon kwace naira milyan 500 da wata dala 500,000 da aka samu a cikin wani asusun ajiyar Yari.
Rukunnan Binciken Da EFCC Ke Wa Yari:
Harkallar Naira Biliyan 300: Yari ya sake shiga hannun EFCC, bayan kotu ta kwace makudan kudaden cikin asusun bankunan ajiyar sa
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, AbdulAziz Yari ya sake shiga wata tsomomuwa a hannun EFCC, inda ta sake gayyatar sa, makonni biyu bayan da hukumar ta sa Babbar Kotun Tarayya ta kwace wasu makudan kudade a cikinn asusun ajiyar sa da ke cikin wasu bankuna.
PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa a ranar Talata Yari ya shafe awoyi masu yawa a hannun EFCC ana sheka masu ruwan zafin tambayoyi.
An dai sake gayyatar sa ne a ofishin EFCC da ke Lagos, inda ya isa wajen karfe 11 na rana, domin amsa gayyatar hukumar.
Majiya ta ce ann gayyaci Yari ne inda ya sha tambayoyi dangane da wani yunkuri da yi na neman karkatar da zunzurutun naira bilyan 300 daga wani banki zuwa wani karamin banki daban.
Duk da an ce ya yi wa jami’an EFCC dogon bayani, majiya ta nuna cewa akwai bukatar a sake gayyatar sa ya koma, domin sun kyale shi ya koma masaukin sa da yammacin Talata din a Lagos.
Kakakin Yada Labarai na EFCC, Wilson Uwujeren, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa tabbas an gayyaci Yari a ofishin su na Lagos, kuma ya amsa gayyatar.
A ranar 26 Ga Janairu ne Babbar Kotun Tarayya ta kwace kudaden asusun ajiyar Yari, saboda kasa bada bayanin yadda ya same su.
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bada umarnin kwac dukkan kudaden da ke cikin asusu daban-daban na tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari.
Kotu ta ce kwace dukkan kudaden ya zama wajibi, saboda tsohon gwamnan, kuma tsohon shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya tsakanin 2015 zuwa 2019, ya kasa yi wa kotun sahihi kuma gamsasshen bayanin yadda ya mallaki makudan kudaden.
Yawancin kudaden dai an dankare su ne a Bankin Polaris, kamar yadda aka fitar da bayanai dalla-dalla.
An kwace masa dalar Amurka 56,056.75 a asusun Polaris Bank, sai kuma naira milyan 12.9 da kuma wasu naira milyan 11.2.
Akwai kuma wasu zunzurutun dalolin Amurka ajiye har dala 301,319.99 wadanda su ma kotu ta kwace.
Sannan an kwace naira 217,388.04, sai kuma wasu dala 311,872.15 da ya boye a Zenith Bank, wadanda su ma kotun ta kwace daga hannun sa.
Babbar Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu, ta ce kotu ta kwace kudaden kamar yadda EFCC ta roki kotun ta yi, tunda Yari ya kasa bada kwakkwaran bayanin yadda ya tara kudaden, a matsayin sa wanda ba dan kasuwa ba.
Yari ya yi gwamnan Zamfara tsawon shekaru takwas, daga 2011 zuwa 2019.
Tun da farko dai ICPC ce ta shigar da kara tun cikin 2019, inda ta shaida wa kotu cewa sun gano inda Yari ya boye wasu makudan kudade. Don haka ICPC ta na bukatar kotu ta kwace kudaden, ko kuma Yari ya je ya yi wa kotu gamsasshen bayanin hanyar da ya bi ya samu kudaden.
Hukumar ICPC a lokacin ta maka Yari kotu tare da wasu kamfanonin sa biyu, wato Kayatawa Nigeria Ltd da kuma B. T. Oil and Gas Nigeria Ltd.
Tun a ranar 16 Ga Agusta, 2019 ce Mai Shari’a Taiwo Taiwo ya bada umarnin a kulle asusun kada a bar Yari ya kara taba ko sisi a cikin kudaden, har sai an ga abin da shari’a ta kaya tukunna.
Lauyan ICPC Osuobeni Akponimisingha ne ya shigar da karar Yari a madadin ICPC.
A lokacin mai shari’ar ya kuma yi wa Yari adalci cewa duk ma wani da ke ganin cewa kudin da ke asusun Yari na sa ne, to ya zo kotu ya bayar da shaida. Amma ba a samu ko mutum daya ba.
ICPC ta ce kudaden da ke asusun Yari duk na sata ne, kudade ne mallakar al’ummar jihar Zamafara da kuma Gwamnatin Tarayya.
Shi dai Yari ya kasa kare yadda aka yi ya tara kudaden, sai dai kawai ya ce wa kotu shi fa tun kafin ya zama gwamna kasaitaccen attajiri ne.