TSINUWA: ‘Yan dandatsa su ka kwace min shafin Facebook, aka tsine wa Deji Adeyanju a ciki – Minista Pantami

0

Ministan Sadarwa Isa Pantami ya yi ikirarin cewa ‘yan dandatsa sun kwace masa shafin Facebook a ranar Litinin, har su ka kutsa ciki su ka yi rubuce-rubucen da ba shi ya yi ko ya bayar da umarnin a yi tsinuwar ba.

Sanarwar Minista Pantami ta zo ne bayan wata tsinuwa ta bayyana a shafin Facebook na Isa Pantami, inda aka tsine wa dan rajin kare dimokradiyya da jama’a, Deji Adeyanju.

Adeyanju ya rubuta wa Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya da kuma Ofishin DSS cewa su binciki zargin alaka da ta’addanci da ake wa Minista Pantami.

Adeyanju ya zura jiki sosai wajen kamfen din ganin cewa Minista Pantami ya sauka daga mukamin sa, dangane da zargin da ake masa.

Tsinuwa Kan Adeyanju A Shafin Facebook Na Pantami:

A karkashin shafin Facebook na Minista Pantami, an bayyana Adeyanju a matsayin makiyin Musulunci, sannan aka tsine masa da Hausa: ‘Allah ya tsine maka albarka”.

To sai dai kuma Minista Pantami ya yi gaggawar rubuta cewa: “Wannan shafi na Facebook di na, wasu ‘yan dandatsa (hackers) sun kwace shi, su ka shiga yi rubuce-rubuce a ciki. Wasu matasa ke kula da shi, ba Isa Pantami ba. Kada kowa ya kula duk wani bayani da aka yi a cikin sa.” Haka Pantami ya rubuta a ranar Litinin da dare.

Tuni dai aka cire rubutun da aka surfa wa Deji Adeyanju tsinuwar.

Binciken da PREMIUM TIMES ta yi ya tabbatar da cewa a e-mel din Isa Pantami aka bude shafin Facebook din: “isapantami@yahoo.com”

Sannan hot-mel din da aka nemi bayanan bude shafin, wato isaaliibrahim@hotmail.com” shi ma ya yi daidai da sunan Minista Pantami a cikin shafin na intanet.

Kakakin Yada Labarai na Minista Pantami, wato Uwa Ibrahim, ba ta amsa wa wakilin mu tambayoyin da ya yi mata ta waya ba.

Share.

game da Author