Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ta kama wata matar aure, Nnenna Egwuagu mai shekaru 29 bayan ta kashe dan kishiyarta da gubar fiyafiya.
Wannan abin tausayi ya faru a kauyen Umulumgbe dake karamar hukumar Udi ranar 9 ga Afrilu da misalin karfe 10 na dare.
Kakakin rundunar Daniel Ndukwe ya sanar da haka ranar Juma’a.
Ya ce ‘yan sanda sun samu labarin aika-aikan da Nnenna ta aikata bayan karar da mahaifin yaron Justine ya shigar a ofishin ‘yan sanda dake 9th Mile.
“Justine ya yi bayanin cewa tun da dadewa yake zargin Nnenna da cin zarafin dansa sai dai Allah bai bashi ikon daukan mataki ba.
Ndukwe ya ce sakamakon binciken da ‘yan sanda suka gudanar sun gano cewa Nnenna ta aikata haka ne saboda yadda mijinta Justine ya daina kula da ita da ‘yarta.
” Ban dirka wa yaron fiyafiya don ya mutu ba, na yi haka ne don yayi rashin lafiyar da mahaifin sa zai kashe makudan kudi a asibiti kafin ya warke kuma sai ya rasu bayan ya sha gubar.
Ya ce fannin gurfanar da masu aikata laifi irin haka za ta ci gaba da bincike a kai.