A turance ana amfani da kalmomin efficacy da effectiveness tamkar ma’anarsu daya. A hausa, efficacy na nufin Ingancin allura. effectiveness kuma na nufin tasiri ko karfin aikin allura. Wata kila kun taba jin yadda ake musayar ma’anar wadannan kalmomin biyu sadda ake amfani da su a turanci wajen kwatanta inganci ko karfin aikin allurar rigakafi.
Zamu fayyace muku banbancin a wannan labarin bisa la’akari da yadda ake amfani da su wajen kwatanta inganci da tasirin allurar rigakafi, domin ana yawan amfani da su wajen bayar da bayanai marasa gaskiya.
Bari mu fara da Public health impact ko kuma Abun da ke da amfani ga lafiyar jama’a. Ana gwada wannan domin tantance dangantakar da ke tsakanin cikakken bayani dangane da batu, da sakamakon da ake samu bayan an bayar da bayanin musamman ta yadda ya shafi lafiyar jama’a. Bayanan da jama’a suke da shi dangane da lafiyarsu kan bayyana a yanayin yadda suke gudanar da rayuwarsu. Ana iya amfani da wannan yawan bullar cuta a al’umma. Ana amfani da hanyoyi biyu wajen tantance wannan. Wato abun da ake iya dangantawa da kuma inganci ko tasiri.
Sau da yawa ana amfani da kalmomin inganci da tasiri (Karfin aiki) a matsayin suna nufin abu daya musamman yadda ya jibanci allurar rigakafi kuma mafi yawan lokuta yadda ya danganci allurar rigakafin COVID-19. Inda a kan yi amfani da su wajen kwatanta karfin aikinsu kuma ba abu daya suke nufi ba.
EFFICACY – INGANCI
Wannan na nufin iya karfin da allurar rigakafi ke da shi wajen kare mutane daga kamuwa da cuta a lokacin da ake gwaji. Wato a lokacin da ake gudanar da bincike, komai shiryawa ake yi sannan akan samar da rukunnan mutane biyu a baiwa rukuni daya maganin da ake so a tantance dayan kuma a basu wani abu daban kafin a duba a ga karfin aikin allurar sannan a kwatanta sakamakon da aka gani daga rukunan biyu.
Allurar rigakafin da ke da karfin kashi 90 cikin 100 a lokacin gwaji alal misali na nufin cewa zai rage yiwuwar kamuwa da cuta da kashi 90 tsakanin wadanda suka karbi allurar rigakafin idan aka kwatanta da wadanda basu karba ba.
EFFECTIVNESS – TASIRI (Karfin aiki)
Tasiri a daya hannun kuma na nufin karfin aikin allurar a lokacin da aka fitar da ita aka baiwa al’umma baki daya.
A cewar wani binciken da D S Fedon, wani mai nazarin cututtuka, ya gudanar, binciken ingancin allura ya kan yi tambayar “shin allurar na aiki?” A yayin da binciken tasirin allurar ke tambayar ko “shin allurar na taimakon jama’a?”
A kan kyautata zaton cewa allurar rigakafi mai inganci sosai zai yi aiki sadda aka kai wa al’umma baki daya amma a zahiri ba lallai ne maganin ya yi tasiri yadda ake bukata ba.
Yanzu da muka ga ma’anar kalmomin biyu, yana da mahimmanci mu lura da cewa idan allura ra nuna tana da inganci a dakin gwaje-gwaje ba lallai ne ta yi tasiri a waje ba. Wannan na nuna mana cewa ingancin allura a lokacin gwaji na iya sa a zuzuta karfin aikin allurar bayan ba haka ba ne a zahiri.
Lokacin da ake gwada allura, akan gyara komai yadda ya kamata, wannan na nufin ba a amfani da wadanda suke da wasu cututtuka na daban ko kuma wadanda ke da lalurar da sai sun sha wa magani a lokacin gwaji saboda gudun lahani.
Haka nan kuma, wadanda suka amince su shiga gwajin, suna wakiltar kadan ne daga cikin sassan al’umma. Misali lokacin da ake gwada alluran COVID-19 ba’a gwada maganin a kananan yara ba amma ana sa ran basu alluran nan ba da dadewa ba.
Idan aka baiwa al’umma allurar rigakafi, abubuwan da suka hada da mutanen da ke shan magani, mutanen da ke fama da wasu cututtuka na daban, shekaru, da yadda aka ajiye allurar da ma yanayin da aka bayar da allurar ga jama’a duk suna iya rage karfin allurar wajen rage kamuwa da cutar.
Ta yaya ke nan za mu gwada tasirin/karfin aikin allurar?
Da zarar aka gwada allura aka gano cewa tana da inganci, wajibi ne a auna karfin aiki ko tasirin ta domin ta haka ne kadai za’a tabbatarwa jama’a mahimmancin amfani da ita. Sannan ta haka ne za’a sami hikimar kirkiro wasu alluran da suka fi wannan.
Shi ya sa yake da mahimmanci a yi bincike dan samun bayanan da za su taimaka wajen fahimtar tasirin maganin. Haka nan kuma ana bukatan bayanai daga wadanda suka karbi allurar rigakafin.
Wadannan bayanai za su hada da lokacin da mutane suka karbi allurar da bangaren al’ummar da ya karba a kowace kasa.
Masu binciken tarihin cutututtuka ko kuma epidemiologists a turance sukan auna karfin aikin allura da abun da suke kira binciken sanya ido saboda akan zabi mutane ne ba tare da an yi amfani da wata ka’ida ba a fara basu magunguna. Alal misali, ana iya sanya ido kan rukunin mutanen da suka karbi allurar rigakafin bayan sun riga sun kamu da cutar, a hada da wadanda ba su taba kamuwa da cutar ba kuma ba a riga an basu rigakafinta ba. Dukkaninsu kuma za’a tabbatar sun fito daga rukunin al’ummar da ake hasashen cewa su cutar za ta fi kamawa. Idan har allurar na da tasiri sosai, za a fi ganin haka a rukunin wadanda basu taba karbar rigakafin ba.
Ba lallai sai allurar rigakafi tana da tasiri sosai kafin ta zama mai amfani ba. Misali allurar rigafin mura tana da tasirin kashi 40 zuwa 60 cikin 100 ne kacal amma kuma tana kare dubban rayuka kowace shekara.
Yaya batun ya ke da alluran rigakafin COVID-19?
Ana kiyasin cewa akwai alluran rigakafin COVID-19 guda 96 wadanda ake kan sarrafawa. A yanzu haka an wallafa sakamakon wucin gadi na wasu bincike guda hudu da aka gudanar a kasidun kimiyya dangane da alluran Pfizer, da Moderna, da AstraZeneca- Oxford da Gamaleya. Bincike uku ne kadai suka bi ta hannun Hukumar kula da Abinci da Magunguna ta Amirka dangane da Pfizer da Moderna da Johnson and Johnson.
Tasiri/karfin aikin Pfizer ya kai kasha 95 cikin 100 Moderna 94 cikin 100 kashi 90 cikin 100 na Gamaleya, kasha 67 cikin 100 na Johnson and Johnson, da 67 cikin 100 na AstraZeneca
A Karshe
Duk da cewa hankula sun karkata ga ingancin allurar rigakafin, fahimtar banbancin da ke tsakanin inganci da tasirin allurar ba a bayyane ya ke ba. Haka nan kuma yadda ake gudanar da binciken a gabatar ya na da dan matsala domin ba a yin la’akari da ko karfin allurar zai iya rage duk hadarin da ke tattare da cutar, iyakacin a duba yawan hadarin da zai iya ragewa. Saboda haka rahotan ya danganci abubuwan da aka duba wanda kuma na iya kawo cikas wajen fahimtar ingancin allurar.
Dan haka ya kamata a fahimci binciken da ake dubawa domin tabbatar da cewa duk wani kwatancen da ake yi ya kunshi duk hujjojin da aka samu daga sakamakon gwaje-gwajen da aka yi yayin da ake bayani kan ingancin allurar
Discussion about this post