Yayin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya garzaya neman lafiyar sa a Ingila, ya bar likitocin Najeriya su na fama da yayin aikin rashin biyan su hakkokin su, shugaban ya dawo ya samu kasar nan cikin gagarimar matsalar wutar lantarki a jihohi 36 da Abuja.
Wannan gagarimar matsalar rashin wuta ta faru ne sanadiyyar matsalar da tashohin karfin lantarkin Najeriya su 18 su ka samu, inda 9 daga cikin su su ka lalace, saura kuma na fama da karancin gas din da ake amani da shi wajen tayar da injinan bada karfin wuta zuwa sassa daban-daban.
Ministan Makamashi Saleh Mamman ne ya bayyana fuskantar wannan babbar matsala a ranar Alhamis, bayan da ‘yan Najeriya su ka fara nuna damuwa da matsalar karancin wutar da ake fuskanta a fadin kasar nan.
“A halin da ake ciki yanzu, manyan tashoshin lantarki takwas sun lalace, amma daya tashar kuma ana yi mata garambawul din da aka saba yi mata ne a kowace shekara.”
Ministan ya kara da cewa, “Ina mai bada hakurin lamarin rashin wutar da kasar nan ke fama da shi. Sauran tashoshi bakwai kuma da ake fama da su, su na fuskantar karancin gas ne, sai kuma wata daya da ita tashar lantarki mai amfani da madatsar ruwa ce, ta na fuskantar karancin ruwa.”
MUN BANI MUN LALACE:
Sunayen Tashoshin Da Su Ka Lalace:
Tashoshin da Ministan Makamashi Saleh Mamman ya lissafa sun lalace, sun hada da tashar lantarki ta Sapele, Afam, Olonrunsogo, Omotosho, Ibom, Egbin, Alaoji da ta Ihovbor. Sai kuma tashar Jebba wadda a halin yanzu ke a rufe saboda aka yi mata kwaskwarimar da aka saba yi mata a duk shekara.
Tashoshin Da Ke Fama Da Karancin Gas:
Tashoshin da ke fama da karancin gas sun hada da ta Geregu, Sepele, Omotosho, Gbarain, Omuku, Paras da ta Alaoji, yayin da tashar Shiroro ke fama da matsalar ruwa.
Duk da yawan jama’ar Najeriya sun kai miliyan 200, har yau karfin wutar da kasar ke da shi bai wuce migawatts 4,000 ba.
Discussion about this post