Farmaki Kan Gidan Kurkukun Imo: Yankin Kudu-maso-Gabas da ya hada da jihohin Abia, Anambra, Enugu da Imo ya dagule tun bayan harin da aka kai wa Gidan Kurkukun Jihar Imo aka saki fursunoni kudan 2,000.
Dama kuma tun kafin wannan, an shafe shekaru ana fafatawa da tsagerun IPOB da sojoji, sannan kuma baya-bayan nan, IPOB sun kafa dakarun tsaro na ESN, wato Eastern Security Network, wadanda hususan ayyukan su ya jibinci korar Fulani makiyaya daga yankin da kuma kashe su, tare da kai wa Hausawa ‘yan tireda hare-hare.
Akalla mahara da su ka dira gidan kurkukun Imo da ke Owerri babban birnin jihar, sun saki fursunoni har 1,844, kamar yadda jami’an gidan kurkukun su ka tabbatar.
Wannan hari dai an zargi tsagerun IPOB, duk da dai kakakin yada labarai na Hukumar Gidan Kurkuku, Francis Enobore ya fitar da sanarwar cewa wasu ‘yan bindiga ne, amma bai furta sunan kungiyar IPOB ba.
“Sun yi nasarar shiga cikin gidann kurkukun da misalin karfe 9 na dare, ta hanyar fasa bango ta baya da nakiya.
Lokacin da ya yi sanarwar, a ce wasu shida sun koma, sannan wasu 35 sun ki ficewa.
Kai Wa Hedikwatar ’Yan Sandan Imo Hari:
Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta tabbatar da cewa tsagerun IPOM ne su ka kai wa Hedikwatar ‘yan sandan jihar Imo hari. Kuma sun zarge su da kai hari gidan kurkukun jihar har su ka saki daurarru 1,844.
Kakakin ‘yan sanda Frank Mba ya ce ba a kashe dan sanda ko daya ba, amma wani ya ji rauni.
Amma hukumar ta dora laifin a kan IPOB da tsagerun tsaron kungiyar wato ESN.
“An kai harin tsakar daren Lahadi, kusan wajewar garin Litinin 5 Ga Afrilu, 2021 wajen karfe 9 na dare” Inji sanarwar kakakin ‘yan sandan Najeriya, wato daidai lokacin da aka kai farmaki gidan kurkukun jihar kenan.
Sufeto Janar Mohammed Adamu ya umarci Kwamishinan ‘Yan Sandan Jhar Imo ya gano wadanda su ka kai farmakin kuma a damke su.
Buhari Ya Yi Tir Da Hare-haren Kurkukun Imo Da Na Hedikwatar ’Yan Sandan Imo:
Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da harin da wasu ‘yan bindiga su ka kai hedikwatar ‘yan sandan jihar Imo da kuma gidan kurkukun jihar, har su ka saki daurarru 1,844.
Tun bayan kai hare-haren dai jami’an ‘yan sandan kasar nan su ka dora alhakin a kan tsagerun IPOB da kuma bangaren tsaron su na ESN.
“A fushin da ya nuna tun da safiyar Litinin, Shugaba Buhari ya jinjina wa kokarin da jami’an tsaro su ka yi wajen hana masu harin kaddamar da kashe-kashe da lalata dukiya.”
Haka sanarwar da Kakakin Yada Labarai na Shugaban Kasa, Garba Shehu ya bayyana a ranar Litinin.
Buhari ya nuna fushinn sa daga Landan inda ya je domin a duba lafiyar sa.
Buhari ya ce wannan farmaki ta’addanci ne, kuma ya gargadi dukkan bangarorin hukumomin tsaron yankin Kudu-maso-Gabas su tabbatar da sun binciko kuma sun kamo wadanda ke da hannu, sannan an hukunta su a kotu kamar yadda doka ta tabadar.
Hare-haren Imo: Gwamna Uzodinma Ya Kafa Kwamitin Bincike:
Gwamna Hope Uzordinma na Jihar Imo ya yi tir da hare-haren da aka kai Hedikwatar ’Yan Sandan Jihar Imo da kuma Gidan Kurkukun Jihar da ke Owerri, babban birnin jihar. Ya ce hare-haren biyu dabbanci ne karara.
Ya yi wannan bayani bayan tashi daga taron Majalisar Tsaron Jihar Imo a Gidan Gwamnati, inda ya tattauna irin barnar da masu kai hare-haren su ka yi.
Dama kuma kafin sannan, sai da gwamnan ya ziyarci dukkan wuraren da aka kai wa munanan hare-haren.
Uzodinma ya ce ya kafa kwamitin da zai binciki lamarin kuma tabbas sai an hukunta dukkan masu hannu a kai hare-haren.
Idan Gemun Dan’uwan Ka Ya Kama Wuta: Jihar Abia Ta Sa Dokar Ta-baci A Wasu Garuruwa:
Ganin yadda lamari ya dagule a jihar Imo, hakan ya sa Gwamnatin Jihar Abia kakaba doka a babban birnin jihar Umuahia, da kuma Aba, birnin kasuwanci na yankin jihohin kabilun Ibo.
An kafa dokar hana zirga-zirgar ce dan lokaci kadan bayan da mahara da aka zarga tsagerun IPOB da ESN su ka kai mummunan farmaki da Hedikwatar ‘Yan Sandan Imo da kuma Gidan Kurkukun Jihar Imo a Owerri, har su ka saki fursunoni 1,844.
Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Abia, John Kalu ne ya sanar da kakaba dokar hana zirga-zirgar a Aba da Umuahia.
Ya ce an hana zirga-zirga daga karfe 10 na dare zuwa karfe shida na safe, har zuwa yadda hali ya yi.
WUTAR FITINA: Yadda ’Yan IPOB/ESN Ke Kokarin Hana Hausawa Zama Yankin Kudu-maso-Gabas:
Hausawa ’yan tireda wadanda ba su san hawa ba, ba su san sauka ba, sun wayi gari a ranar 25 Ga Janairu, 2021 sun hango wani gungun ’yan iskan matasan kabilar Igbo da ke kiran kan su Jami’an Tsaron Kudu maso Gabas, wato ‘Eastern Security Network’.
Sun ciko motoci hudu, kowa dauke da bindiga, kuma kowanen su ya rufe fuskar sa. Su na isa tsakiyar da cincirindon Hausawa su ke a kasuwar, sai su ka fara bude masu wuta, tare da banka wa kasuwar, bangaren da Hausawan su ke wuta.
Wani mai suna Ahmadu Ali, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa, “mu dai kawai sai mu ka hango wasu motoci hudu dauke da ’yan ESN sun biyo hannun da ba na su ba, kuma sun tunkaro mu gadan-gadan. Su ka bude mana wuta pa pa pa pa pa, babu kakkautawa.”
Ali ya ce nan take su ka kashe mutum uku, kuma wani mai suna Salisu Sali su ka kone shi. Ya ce sauran Hausawa ’yan tireda kuma sun tsere ne ta hanyar shiga filin wasa na Orlu, amma yawancin su duk akwai harbi a jikin su.
Ya bayyana sunayen wadanda aka kashe din cewa akwai Usman Ali, Mohammed Rabiu da kuma Nura Muhammadu.
Nura dai dan asalin Jihar Sokoto ne, amma sauran ukun ’yan Jamhuriyar Nijar ne.
PREMIUM TIMES ta samu munanan hotunan wadanda aka bindige din kwance male-male a cikin jini.
Sannan kuma jaridar nan ta na da hotun lokacin da kasuwar ke cin wuta.
Wani mai suna Golden Marvin ya tabbatar da cewa ’yan ESN ne su ka yi aika-aikar saboda akwai sunan kungiyar ta su rubuce a jikin motocin su.
Su ma jami’an ’yan sanda sun tabbatar da haka, domin sun bayyana cewa sun kama wasu da ake zargin sun aikata aika-aikar.
Yayin da wasu mutane da dama sun shaida wa wannan jarida cewa sun ga lokacin da ake banka wa kantinan Huasawa wuta tare da harbin su da bindiga, an kuma bayyana cewa ’yan sanda na tsaye na kallo, amma suka kasa kai masu dauki.
Ali yac e a yanzu Hausawa ba su iya yin kasuwanci a kasuwar.
Bayan wancan hari da aka kai wa Hausawa, akalla harsashe ya samu mutum 10 cikin su har da sojoji hudu, wadanda duk sun mutu a rikice-rikice daban-daban a Orlu.
Kungiyar Tsagerun IPOB su ka kafa ESN domin fatattakar Fulani kamar yadda ake kan yi a wasu sassan jihohin Kudu maso Yamma.
Yadda Aka Afka Wa Hausawa Da Harbi A Orlu:
Majiya ta ce lamarin ya faro ne daga wata dambarwa tsakanin tsageran ESN da kuma sojoji da ’yan sanda a bangare daya, ba su daya ko sau biyu ba. Amma dai sojoji sun kai masu wani samame kafin ranar 25 Ga Janairun da ESN su ka kai wa Hausawa Hari.
Sojojin sun kai masu samame ne a cikin dajin da su ka kafa sansani.
“To su kuma tsagerun sai su ka fito da nufin yin ramuwar-gayya a kan sojoji da ’yan sanda. Sun yi kokarin kai wa wani ofishin ‘yan sanda hari amma aka kore su.
“Daga nan ne kuma su ka tunkari Hausawa a kasuwar Orlu, su ka huce haushi a kan su. Su ka kashe mutum hudu, kuma su ka kone masu kantinan su.”
Kafin wannan kashe-kashen kuma, su ma ‘yan sand aba su tsira ba daga kisan-gillar da tsagerun IPOB, reshen ESN su ka rika yi masu, bas au daya ko sau biyu ba.
Jami’an tsaro sun gano cewa tsagerun sun kafa sansanin ne a cikin daji wajejan Okporo and Umutanze.
Wani da aka yi hira da shi da ya nemi a sakaya sunan sa, ya bayyana cewa kafin sojoji su tarwatsa su, a samamen da su ka kai masu kafin ranar 25 Ga Janairu, sai da tsagerun na ESN su ka gagari jam’an ’yan sanda, har su ka bindige masu jami’i guda daya.
Wannan dalilin ne ya sa aka tura masu sojojin da su ka tarwatsa su, wanda su kuma hakan ne ya sa su ka yi daukar fansar huce haushi a kan Hausawa.
Ba wani abu ke kara ruruta IPOB da ESN ba, sai hankoron da wasu matasan Inyamirai key i domin ganin sun kafa Biafra, mafarkin da Ojukwu dan tawaye ya kasa cikawa a lokacin Yakin Basasa.
Nnamdi Kanu ya sake farfado da wannan mafarki a cikin 2012, inda ya kafa kungiyar IPOB.
Wani mazaunin Orlu mai suna Aloysius da ya ce bai so a bayyana cikakken sunan sa, ya nuna cewa al’ummar garin na cikin rashin jin dadin irin hargitsin da ake samu ya na tashi tsakanin tsagerun matasan da kuma sojoji da ’yan sanda.
Amma kuma ya nuna cewa, “A bangare daya mu na fama da Fulani ’yan bindiga a cikin kauyuka sannan kuma siyasar gwamnatin Najeriya ta maida yankin Kudu maso Gabas saniyar-ware.’’
Masana na ganin cewa matasan kabilar Igbo na kai wa jami’an ‘yan sanda hari ne domin su samu makamai, saboda ba su da kan iyakar da za su rika samun makamai daga makwautan kasashe.
Sannan kuma ana ganin lamarin na su ba zai yi tasiri sosai ba, saboda ba su da jimirin yin aika-aika kamar yadda Fulani ke yi a Arewacin kasar nan, inda su ke zaune a daji dindindin.
Kuma har ila yau, yankin da kabilar Igbo ba shi da dazukan da za a rika boyewa ana sunkuru, ko hare-haren sari-ka-noke.