TASHIN HANKALI: Korona na neman durkusar da Indiya, dubbai na mutuwa a rana, sama da 300,000 na kamuwa a kullum

0

Indiya ta hadu sabon tashin hankalin fantsamar cutar korona da ya sake darkakar kasar a karo na biyu.

Rahotanni a ranar Litinin sun tabbatar da cewa a cikin sa’o’i 24 da su ka gabata, korona ta kama mutum 352, 991.

Kididdiga ta kuma tabbatar da cewa annobar ta kashe mutum 2,812 a cikin kwana daya.

An kuma jera kwanaki biyar kenan a kullum wadanda ke kamuwa da cutar a Indiya su na haura mutum 300,000.

Ya zuwa yanzu dai korona ta kashe mutum 195,123 a Indiya, yayin da fiye da mutum miliyan 17.3 ne su ka kamu da cutar ta korona a fadin kasar.

Kasashen Amurka, Birtaniya, Faransa, Jamus da Isra’ila duk sun bayyana cewa za su tura agajin kayan a cikin gaggawa zuwa Indiya.

Firayi Minista Narendra Modi ya bayyana cewa, “annobar korona ta jijjiga Indiya.’ Amma ya kara da cewa gwamnatin kasar na kokarin dakile annobar.

Yayin da Shugaba Biden na Amurka ya bayyana aikawa cikin gaggawa da sinadarin hada rigakafin ‘Covishield’ domin kara yawan hada alluran korona a Indiya, Birtaniya ta ce za ta aika da kayan kula da masara lafiya da su ka hada da tukanen shakar iska da sauran kayayyaki masu yawa a cikin gaggawa.

Tarayyar Turai, Jamus da Isra’ila duk sun ayyana aikawa da taimakon kayan magani zuwa Indiya cikin gaggawa.

Share.

game da Author