Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa sojoji dake sintiri a dazukan Kaduna sun shaida mata cewa sun ceto wasu daga cikin daliban da mahara suka yi garkuwa da su a Kaduna.
Idan ba a manta ba, mahara sun sace dalibai 39 daga makarantar Koyan aikin gona da gandun dazuka, dake Afaka, karamar hukumar Igabi, jihar Kaduna.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna Samuel Aruwan ne ya bayyana haka a sako da ya saka a shafinsa na Facebook ranar Litini.
Aruwan yace tuni har an garzaya da diban asibiti domin a duba lafiyan su.
Ya kara da cewa gwamnati za ta bada cikakken bayani game da abinda ya faru nan ba da dadewa ba.