Kungiyar Bin Diddigin Gudanar da Ayyukan Gwamnati Bisa Ka’ida (SERAP), ta maka Shugaba Muhammadu Buhari kotu, “saboda ya kasa ko kuma ya kauda kai daga binciken zargin salwantar naira N3,836,685,213.13 wadanda aka ware domin ayyuka a Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya.
“Haka kuma wani bangare na kudin an fitar da su ne domin yin wasu ayyukan inganta kiwon lafiya a Asibitocin Koyarwa, Cibiyoyin Inganta Lafiya da kuma Hukumar NAFDAC.
“Sai dai kuma maimakon a gudanar da ayyukan, an yi zargin ko dai sun salwanta, ko kuma an sace, ko an karkatar da su, kamar yadda wani binciken kudaden 2018 da aka fito da shi kwanan nan ya tabbatar da salwantar kudaden.
“Ofishin Babban Mai Binciken Kudade na Tarayya, wato ‘Audutor General of the Federation’ ne ya fitar da sakamakon binciken.” Inji SERAP.
An shigar da wannan kara a kotu a daidai lokacin da ake sa-to-sa-katsi dangane da tafiyar Shugaba Muhammadu Buhari Ingila domin a duba lafiyar sa.
Buhari ya tafi Ingila ganin likita kwana daya kafin likitocin da ke horon kwarewa su tafi yajin aiki, saboda rashin biyan su albashi, neman kara masu alawus din shiga-hatsari da saida rayuwa da kuma kukan kara masu ingantattun kayan kariya yayin aikin kula da masu fama da cutar korona.
Wannan tafiya yajin aiki ta jefa miliyoyin ‘yan Najeriya cikin gagarimar matsalar kula da marasa lafiya a asibitocin kasar nan.
Cikin kwafen wannan karar da aka shigar din mai lamba FHC/ ABJ/CS/433/2021, a cikin makon da ya gabata, an nemi Babbar Kotun Tarayya, ta yi amfani da karfin shari’a (order of mandamus) ta tilasta Shugaba Buhari ya binciki yadda naira biliyan 3.8 su ka salwanta a Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya.
Sannan kuma a tilasta wa Buhari ya binciki irin barna, cuwa-cuwa, harkalla, baruwa da ragargazar kudaden da ake yi a Asibitocin Koyarwa na Gwamnatin Tarayya da Cibiyoyin Inganta Lafiya na Kasa, har ma da Hukumar NAFDAC.
SERAP ta kuma bayyana cewa lallai tilas bayan an kammala bincike, to a gaggauta gurfanar dawadanda su ka sace kudaden kotu, koma a hukunta su kamar yadda doka ta tanadar. Sannan kuma a kwato kudaden daga hannun su.
Kungiyar tace sace wadannan makudan kudade ya jefa miliyoyin ‘yan Najeriya cikin halin rashin ingantacciyar lafiya a kasar nan.
Rashin gudanar da bincike da kin kwato kudaden ya nuna gwamnatin Buhari ta karya doka kuma ta jefa rayuwar milyoyin ‘yan Najeriya cikin hatsari, inji SERAP.
Wadanda lauyoyin SERAP, Kolawole Oluwadare da Opeyemi Owolabi su ka hada su ka maka kotu tare da Buhari, sun hada da Ministan Shari’a Abubakar Malami, sai kuma Ministan Harkokin Lafiya, Osagie Ehanire.
SERAP ta kuma nuna damuwa dangane da yadda dan karen sata da wawurar kudade su ka hana talakawan Najeriya cin moroiya da amfanar makudan kudaden da gwamnati ke cewa ta na kashewa wajen kula da lafiyar jama’ar kasar nan.
Tuni dai manyan jami’an gwamnati tun daga shugaban kasa su ka yi watsi da asibitocin Najeriya, su ke tsallakawa kasashen waje neman magani.