SAKON SARAKI GA BUHARI KAN MATSALAR TSARO: Ka nemi taimako, matsalar nan ta fi karfin ka

0

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya roki Shugaba Muhammadu Buhari ya tashi tsaye ya nemi taimako ko daga ina domin a shawo kan matsalar tsaron da ta zama tamkar gobarar-daji a fadin kasar nan.

“A mummunan halin da kasar nan ke ciki a yanzu, ya fa wuce Shugaban Kasa ya yi zaune a fadar sa ya na yin tir ko Allah-wadai idan an kai hare-hare ko an yi kashe-kashe. Kuma mun gaji da karanta sanarwa ga manema labarai daga Fadar Shugaban Kasa.

“Ina roko ga Shugaban Kasa ya tashi gaba-gadi ya tarbi wannan gagarimar matsalar munanan tashe-tashen hankulan da su ka buwayi kasar nan, har su ke neman kacalcala kasar gaba daya.

Haka Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya bayyana, ranar Talata, a Abuja.

Saraki na nuna damuwar sa ce dangane da irin tashe-tashen hankulan da su ka faru a kasar nan, a sassa daban-daban cikin kwanaki biyu kacal.

Ya yi magana kama daga hare-hare da yake-yaken ta’addancin Boko Haram, tarzoma a sassan kasar nan da kone-konen dukiyar gwamnati da kisan jami’an tsaro, yawaitar masu garkuwa da mutane da sauran tashe-tashen hankulan da ke ci gaba da tashi.

Hususan ya nuna damuwa dangane da rahoton bullar Boko Haram a Karamar Hukumar Shiroro, inda manyan tashashon bada wutar lantarkin Najeriya su ke.

Wannan abu inji Saraki babban tashin hankali ne, ganin cewa Gwamnan Jihar Neja da kan sa ya ce Gwamnatin Tarayya ta kasa tabuka komai dangane da bullar Boko Haram a jihar Nej, da sauran matsalolin hare-haren ‘yan bindiga da Neja ke fama da su.

“A ce dai Boko Haram sun yi kaka-gida a Karamar Hukumar Shiroro, cikin jihar Neja, har sun kafa tuta a karamar hukumar da manyan tashoshin lantarkin Najeriya su ke, kuma kasa da kilomita 200 daga babban birnin tarayya, Abuja, to ba karamin tashin hankali ba ne.” Inji Saraki.

Saraki ya kuma nuna damuwa kan harin da Boko Haram su ka kai wa sojojin Najeriya a Mainok, cikin Jihar Barno a ranar Lahadi da kuma hare-haren da ke faruwa a jihohin Kudu-maso-Gabas.

Buhari Ka Tashi Ka Nemi Taimako, Shantakewar Ka Ta Yi Yawa -Saraki:

A cikin sanarwar da Saraki ya fitar, ya nuna cewa Buhari ya ajiye girman kai ko taurin kai ko lusaranci, ya tashi tsaye ya nemi taimako ko ma daga ina, matsawar yin hakan zai iya shawo kan guguwar rashin tsaron da ta tirnike Najeriya.

“Bisa dukkan alamu Shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC na matukar bukatar taimako. Gaskiya matsalar ta sha kan su, ruwa ya shanye iyar wuyan su. Su na bukatar dauki daga kowa da kowa.

“Don haka ina kira ga Shugaba Buhari ya nemi taimako ko ma daga ina. Domin ya na cikin mawuyacin halin da kasar nan ke ciki. Wannan matsalar ta fi karfin gwamnatin Buhari.” Inji Saraki.

Share.

game da Author