SAKO GA MA’AIKATAN KANO: Gwamnatin Ganduje ba za ta iya biyan albashin watan Maris gaba daya ba – Kwamishina

0

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana wa ma’aikatan jihar cewa ba zai yiwu ta biya cikakken albashin watan Maris cif-cif ba, saboda karancin kudin da jihar ta karba daga Gwamnatin Tarayya.

Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano Muhammad Garba ne ya bayyana hana, a madadin gwamnatin jihar, inda ya bayyana cewa an samu karancin kudaden da jihar ke karba daga gwamnatin tarayya a watan Maris.

Kafafen yada labarai a jihar, har da jaridar Daily Trsut sun ruwaito Kwamishina Garba na cewa, “karancin kudaden shiga daga gwamnatin tarayya ya sa da wahala gwamnati ta shigar da sabon tsarin biyan alabashi.”

Kafafen yada labari sun ruwaito Kungiyar Kwadago Reshen Jihar Kano ta bai wa gwamnatin jihar wa’adin kwanaki bakwai cewa a daina “cirewa da yanke wa ma’aikata kudaden albashi ba bisa ka’ida ba.”

Shugaban NLC Reshen Jihar Kano, Kabiru Minjibir ne ya bayar da wannan wa’adin, bayan tashi daga wani taro da shugabannin kungiyar su ka yi a ranar Juma’a.

Kabiru ya ce idan ba a daina yanke masu albashi ba har zuwa ranar 6 Ga Afrilu, 2021, to ranar 7 Ga Afrilu tabbas za su tafi yajin aiki.

Sai dai kuma a jawabin Kwamishina Muhammad Garba, ya bayyana cewa a watan Maris Jihar Kano ta karbi naira 12, 400,000,000 (biliyan 12.4) daga Gwamnatin Tarayya.

“Daga cikin kudaden, jiha ta dauki naira biiyan 6.1, ta bai wa Kananan Hukumomi 44 naira biliyan 6.3.”

A kan haka sai Garba ya bayyana cewa idan jihar Kano na so ta biya gaba dayan albashin, to sai ta kara cika wasu biliyoyn nairarorin da a yanzu ba ta da su.

Share.

game da Author