Rundunar sojin Najeriya na yada tsoffin hotuna tana ikirarin yin nasara kan ‘yan ta’adda – Binciken DUBAWA

0

Zargi– Rundunar sojojin Najeriya ta wallafa hotunan da ke nuna wasu motocin da aka lalata, bindigogi, da harsasan da aka anso daga hannun kungiyar ISWAP dake Damasak, yankin arewacin jihar Borno.

Ranar juma’a 16 ga watan Afrilu, rundunar sojin Najeriya ta wallafa wani rahoto a shafinta na twitter mai adireshin (HQNigerianArmy) inda ta ce ta yi nasara kan kungiyar ‘yan ta’addan ISWAP da ke Damasak, jihar Borno yankin arewa maso gabashin Najeriya. Sojojin sun wallafa hotunan da ke nuna motocin da aka lalata da bindigogi da harsasan da suke zargi na ‘yan ta’addan ne.

A wani rahoto mai taken “Yadda babban kwamandan ISWAP da mayakansa suka gamu da karshensu wajen kai harin ramako a Damasak”, sojojin Najeriyan sun ce “‘yan ta’addan sun je rama kisar da aka yi wa manyan kwamandojinsu guda 12 a karamar hukumar Mobbar bayan da aka shafe mako guda ana dauki ba dadi da su ta sama da kasa.”

Haka nan kuma a shafin sojojin na Facebook, rahoton wanda kakakin rundunar sojojin Birgediya Janar Mohammed ya sanyawa hannu ya ce nasarar da suka yi kan ‘yan ta’addan sakamakon tsarin da suka yi amfani da shi ne wajen kai hare-hare ta sama da ta kasa a yankuna da dama na yankin arewa maso gabashin kasar.

Sanarwar ta kuma kara da cewa: “Wani babban kwamandan ISWAP, Bukar Gana Fitchmeram wanda ake wa inkiya da Abu Aisha da mayakansa da dama wadanda suka je daukar fansa a Damasak sun rasa rayukansu sakamakon harin dakarun Najeriya ranar alhamis. ‘yan ta’addan wadanda aka bude musu wuta ba kakkautawa sun yi kokarin kai hari a wurare biyu, wato Gajiram da Damasak amma ba su kai labari ba.

“Hare-haren da aka kai ta sama a Tudun Wulgo, Zari, da Tumbun Alhaji, da Kusuma da Sigir a Ngala da Arijallamari a Abadam da Marte da yankuna a karamar hukumar Ngala su ne suka kai ga mutuwar babban jagoran ISWAP. Kwamandojin da suka mutu a harin sun hada da Mohammad Fulloja, Ameer Mallam Bello, Ba’a Kaka Tunkushe, Abu Muktar Al – Ansari, Ameer Abba Kaka, Abu Huzaifa, da Ameer Modu Kwayen a yayin da Goni Mustapha wanda shi ne limamin ISWAP ya kubuce da raunin bindiga.

Dakarun yakin kasa da hare-haren da aka kai ta sami ranar 6 ga watan Afrilu sun kuma kai ga hallakar wasu shugabanin kungiyar ta ISWAP guda biyu wadanda suka hada da Abu-Rabi da Muhammed Likita da kuma wadansu da dama daga cikin dakarunsu da masu tsaro a yankunan Kusuma, Sigir a Ngala da Arijallamari a karamar hukumar Abadam.

Dakarun da ke karkashin shirin lafiya dole wadanda suka kai hari ta sama sun lalata gidan ajiyar makaman ‘yan ta’addan.

A daren asabar 10 ga watan Afrilu wasu kwamandojin ‘yan ta’addan guda uku wadanda suka hada da Ameer Umar da Abu Ubaida da Abu Salim sun gamu da gamonsu a wani harin kwanton baunar da dakarunsu suka kai, a kusa da yankunan Wulgo/Logomani da kewaye, duk a kan iyakar Kamaru, a yayin da suke kokarin kai hari kan ‘yan garin domin su sace shanu.

Munanan hare-haren da aka kai sansanonin ISWAP ne ya tilastawa wadanda suka rayu zuwa neman dauki na abinci da magunguna domin wadanda suka yi rauni.

Haka nan kuma ranar 11 ga watan Afrilu hare-haren dakarun Najeriya ya kashe ‘yan ISWAP/Boko Haram cikin motoci biyar masu sulke a Damasak.

Harin ya kashe wasu daga cikin ‘yan ta’addan kusa da ke buya kusa da Katanga, a yayinda wasu kuma suka gamu da nasu ajalin lokacin da suke satan kayayyakin abinci a dakin ajiyar ofishin Majalisar Dinkin Duniya da kuma magunguna da motar asibiti. To sai dai sojoji uku da fararen hula sun hallaka lokacin da ake kona wadansu daga cikin gidajen da ke cikin garin.

Wadansu daga cikin ‘yan ta’addan ne suka samu suka shiga cikin gari suka kona wasu wurare suka kuma yi sata kafin suka tsere. Ya kamata mu tuna cewa an kai hari kan Damasak sau da yawa sai dai bai yi tasiri ba. Dakarun sun ce ba su yi kasa a gwiwa ba duk da munafincin masu zuwa su tseguntawa kungiyoyin ‘yan ta’addan bayanan sirrin da suke da shi dangane da wuraren buyansu da sadda za su kai hari.

Tantancewa

Da DUBAWA ta binciki hotunan da sojojin suka wallafa a shafukan Google da Twitter, ta gano cewa an yi amfani da hotunan a watan Maris 2021 a shafukan sada zumunta. Wani mai amfani da shafin twitter mai suna Calibre Obscura (@CalibreObscura) ne ya wallafa hotunan yana danganta su da wani harin ISIS da ya afku a baya a Damasak, Jihar Borno.

Wani shi ma wanda ya baiwa shafinsa sunar “Arms Research and Occasional effortposter” ya yi amfani da hoton ranar 15 ga watan Maris 2021: inda ya ce “bayan da ISIS ta kai hari #Damasak an wallafa hotunan bindigogi kirar AK 47 guda tara da RPG-7 da NSV HMG wadanda sojojin Najeriya suka gano. Kawo yanzu ba a san ainihin mai su ba. Ko da shi ke ISIS na zargin mutane 12 sun mutu amma babu shaida.

Sai dai ranar juma’a 16 ga watan Afrilu 2021 kwanaki kasa da wata guda da wallafa wadannan hotuna, rundunar sojin Najeriya ta sake wallafa su tana ikirarin ta kashe kwamandojin kungiyoyin Boko Haram da ISWAP guda 13.

A Karshe

Hotunan da Sojojin Najeriya suka wallafa ranar 16 ga watan Afrilun 2021 yayin da ta ke kwatanta nasarar da ta yi kan kungiyar ISWAP tsoffi ne. Wadannan hotunan sun riga sun bayyana wata guda kafin nan, ranar 15 ga watan Maris 2021 suna nuna hujjojin da suka shaida harin ISIS a Damasak, jihar Borno.

Share.

game da Author