Sanata Shehu Sani ya bayyana yadda ta kwaranye tsakanin sa da wani korarren ma’aikacin gwamnatin Jihar Kaduna, wanda kwanan nan ya kira shi ya na yi masa korafin Gwamnatin Nasir El-Rufai ta kore shi daga aiki.
A Shafin tsohon sanatan na Facebook, Sani ya bayyana cewa, “Shekaru biyu da su ka gabata, wani ma’aikacin gwamnatin Jihar Kaduna ya kira ni ta waya, ya rika yi min arashi da habaici ya na dariya, wai sun kayar da ni zabe, sun yi mani ritaya daga siyasa. Ni kuma na yi masa addu’a da fatan alheri.
“To kuma cikin makon da ya gabata, sai wannan ma’aikacin dai ya sake kira na ya nay i mani korafin cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ta sallame shi daga aiki. Ya rika ce min an yi masa rashin adalci. Nan ma dai na yi masa addu’a, na yi masa fatan alheri.”
Shehu Sani dai ya yi wannan bayani ne a shafin sa na Facebook, dangane da kakkabar ‘ya’yan kadanyar korar ma’aikata birjik da Gwamnatin El-Rufai ke yi a jihar Kaduna.
Shi dai gwamnan ya fito ya yi korafin cewa kusan fiye da kashi 90 na makudan kudaden da jihar Kaduna ke karbowa daga kason gwamnatin tarayya a duk karshen wata, su na tafiya ne wajen biyan albashin wasu ‘yan tsirarun ma’aikatan da ko da su ko babu su aikin gwamnati zai iya gudana a jihar Kaduna.