Ramadan : Sarkin Karaye yayi kira a tausayawa talaka

0

Maimartaba Sarkin Karaye Ibrahim Abubakar yayi kira ga masu hannu da shuni dasu kara taimakon da suke yi wa talakawa a cikin wannan watan Ramadan, mai alfarma.

Maimagana da yawun masarautar ta karaye, Haruna Gunduwawa, yace sarkin yayi kiran ne a fadarsa dake Karaye yayin jawabin ganin watan Ramadan a daren litinin. Yace ciyar da marasa karfe a watan azumi yanada lada mai tarin yawa.

Sarkin ya kuma yin kira ga al’umma dasu bada himma wajen addu’o’i kan jagoranci nagari da wanzuwar zaman lafiya a Najeriya.

Sarkin ya kuma yin kira ga al’ummar musulmi da suyi koyi da koyarwar addini wajen riko da gaskiya da amana da kuma hakuri da juna a cikin wannan watan Ramadan mai alfarma.

A wani cigaba, Sarkin ya nada Yunusa Yusuf, a matsayin limamin masalacin Juma’a na garin Daburau dake karamar hukumar Madobi.

Haka kuma an sanar da Suleiman Haruna da Sa’adu Saleh Dare-mudu a matsayin na’ibin liman na daya dana biyu.

Sarki Abubakar ya kuma nada Malam Yusuf Ali a matsayin na’ibin limamin masalacin Juma’a dake garin Kubarachi a karamar hukumar ta madobi.

A karshe, sarki yayi kira ga malamai da su kasance masu biyayya kuma su jajarce wajen yi wa kasa da shuganbanni addu’a.

Share.

game da Author