RAMADAN: Babu buda baki, Itikafi an kuma rage yawan raka’o’in Taraweeh a masallatan Makka da Madinah

0

Mahukunta a kasar Saudiyya sun sanar da rage yawan raka’o’in sallar Taraweeh daga 20 zuwa 10 a Azumin Ramadan din bana.

Bayan haka kuma za mahukuntan sun sanar cewa ba za ayi Itikafi a masallatan biyu ba.

Sarki Salman na Saudiyya ya bayar da umurnin haka kamar yadda jaridar Saudi Gazette tavruwaito.

Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito cewa Sheikh Abdul Rahman Al-Sudais, wanda shine shugaban da ke kula da masallatan biyu, ya ce za a rage yawan raka’o’in zuwa 10 daga 20 da aka saba yi.

Sannan za a yi Sallar ne bisa bin ka’idojin da aka gindaya na kariya daga kamuwa da yada cutar Korona.

Al’umman musulmi a duniya za su tashi da Azumi ranar Talata in Allah ya kaimu.

Za a kwashe kwanaki 29 ko 30 ana ta Ibada ga Allah.

Share.

game da Author