Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu Alaikum
A wannan lokaci da muke ciki naga an kaddamar da rabon shinkafa da kayan hatsi na tsohon gwamnan jihar Legas, wato Bola Ahmed Tinubu, Kano. Haba ‘yan uwana Kanawa, ‘yan halal, irin albarka, don Allah kar ku bamu kunya mana!
A hotuna da bidiyoyi da suka bazu a kafafen sada zumunta, wato soshiyal midiya, mun ga mutane da buhuhunan shinkafa mai rubutun ‘JAGABA – Asiwaju Bola Ahmed Tinubu’ ana raba masu, suna turmutsitsi da wasoso, suna turin juna.
Wata majiya mai tushe ta tabbatar mani da cewa lallai gidauniyar Tinubu ce (wato Tinubu Foundation), sune suka jagoranci raba wannan kayan abinci.
Duk wannan al’amari, yana biyo wa ne bayan rade-radin da ake yi cewa Bola Tinubun yana shirin fitowa takarar kujeran shugaban kasa ne a 2023.
To duk ma dai ko mene ne, mu babu abunda zamu ce illa Allah waddai da wannan mataki, na kokarin nuna wa duniya cewa, al’ummar arewa mayunwata ne. Domin idan ba’a manta ba, shi wannan mutum da ma yace shi yana da farashin ‘yan arewa, to wannan shine ya fara nuna wa duniya!
Idan ba rainin wayo ba, don Allah Tinubu ya taba rabon kayan azumi a arewa, a shekarun baya da muka fito?
Har a lokacin da aka kulle mutane saboda cutar annobar korona (lockdown), a lokacin da mutane suke neman agaji da dauki, da taimako, don Allah kun taba jin Bola Tinubu ya aika da taimako a taimakawa ‘yan arewa?
Wato sai a yanzu da yake neman goyon baya, da kuri’un ‘yan arewa, sannan zai tafi da munafuncin sa, yana raba wai shinkafar azumi ko?
Shin yau ne aka fara yin azumi a Najeriya, ko a yankin mu na arewa? Me yasa a can baya bai bayar da gudummawar shinkafar azumi ba sai yanzu da ake so a yaudari al’ummah?
Don Allah jama’ah ku kalli irin yadda ‘yan kudu suke yin rubuce-rubuce, suna yi muna dariya, akan wannan rabon shinkafar Tinubun!
Don Allah kalli yadda aka wulakanta matan mu, da al’ummar mu! Aka ci mutuncin jama’ah, suna ta gogoriyo da ture-ture, wai domin karbar shegiyar shinkafar Tinubu, marar albarka! Haba jama’ah, yanzu don Allah har al’amarin mu ya kai ga haka ne?
Me yasa bai tafi legas yayi haka ba? Wato sai a arewa ko, inda suka mayar mayunwata ko?
Mu dai wallahi babu abunda zamu ce illa, Allah ya isa! Allah ya isa!! Allah ya isa!!!
An jefa al’ummar mu cikin kunci da yunwa da talauci, da damuwa, har sun kai matakin da duk wani kare da doki yazo masu da shirmen sa zasu saurare shi!
Idan ba haka ba, don Allah waye Tinubu?
Kuma ka duba ka gani, sai aka yi amfani da Kano, garin bayin Allah, salihai, don a yaudari al’ummah.
Wallahi wannan al’amari, kalubale ne a wurin dukkanin manyan arewa, da dukkanin ‘yan siyasar arewa! Domin abunda wannan yake nunawa, kuma yake fassarawa duniya, shine, wato kun manyan mu, kun mayar da mu almajirai, mayunwata, matalauta, shine za’a rinka rabawa matayen mu abinci ko, suna turmutsitsi wurin karba? Idan ba haka ba, to don Allah me wannan yake nufi?
Wallahi kwana nan, ko wata daya ba’a yi ba, na zagaya, nayi tattaki, nayi rangadin gani da ido, na tafi jihar legas, da jihar Ikiti, da jihar Osun, da jihar Ogun, na ga mutanen nan duk suna zaune lafiya, suna cikin yalwa da wadata, da annashuwa, amma abun bakin ciki shine, da zarar ka dawo yankin mu na arewa, nan ne zaka tarar da rashin tsaro da sauran matsaloli sun yi muna katutu!
Don haka wallahi ‘yan uwana, ‘yan arewa, ina kiran da ku natsu da kyau, domin muna nan akan bakan mu, babu-gudu-babu-ja-da-baya, mun dauki alkawari, sai mun bayyanawa al’ummar mu gaskiya, tsakanin mu da Allah!
Tinubun nan fa suna sane cewa ba ya da koshin lafiyar da zaya iya rike kasar nan, har shi yasa ma yake yawan katobara da sambatu wurin magana. Sannan idan yana tafiya fa har rike shi ake yi, don kar ya fadi, idan ba haka ba faduwa zai yi. Suna sane cewa muna zargin sa da mummunan dabi’a ta nuna kabilanci. Idan kuwa ba haka ba, su rantse da Allah cewa, babu makudan kudaden sa wurin tafiyar da kungiyar yarbawa zalla ta OPC, da Amotekun da Afenifere. Kuma suyi rantsuwa da Allah cewa, dan iskan nan Sunday Igboho, mai cin mutuncin arewa da ‘yan arewa, sannan mai fafutukar raba Najeriya, mai fafutukar kafa kasar yarbawa ta Oduduwa, su rantse cewa ba yaron Bola Tinubu ba ne. Sannan su rantse cewa Ganiyu Adams ba yaron Bola Tinubu ba ne!
Mutumin nan idon sa a rufe yake da son mulki, shi yasa zai kashe makudan kudade ya nema, idan ya samu kuwa zai yi yadda yaga dama, domin zai ga cewa sayen mulkin nan yayi da kudin sa, don haka dole kokari zai yi yaga cewa yaci riba. Sannan wasu miyagun mutane daga cikin mu, suna nan, a shirye suke, ko iyayen su suna iya sayar wa, in dai har zasu samu kudi!
An kashe ‘yan uwan mu, hausawa da fulani, mutanen arewa a yankin su, amma mutumin nan bai nuna alhininsa a kai ba, kuma bai nuna wata tsawatarwa ga mutanansa masu aikata wannan danyen aiki ba. Mutumin nan ya wulakanta mu, ya nuna cewa dan Arewa yana da farashi, wato kana iya sayensa bisa bukatarka. Dama a can baya, wasu ‘yan uwan sa sun taba cewa, ‘yan arewa kamar kaji suke, da ka watsa masu abinci, to zasu bi ka suna wasoso, kuma suyi maka duk abunda kake so!
Mutumin nan, duk duniya ta shaida cewa, a baya yayi da’awar raba kasar nan, ya nuna cewa shi bai yarda da zaman Najeriya kasa daya ba, amma wai a haka, shi shugabancin kasar nan yake so. Haba Tinubu, kasar da baka yarda da ita ba kuma?
Da wannan nike cewa, idan kunne yaji…
Ya Allah, ina rokon ka, ka bamu shugaba nagari, kuma na kirki a 2023, amin.
Daga karshe, ina kira ga dukkanin ‘yan arewa, da cewa wallahi mu shiga taitayinmu!
Wannan mutum mai suna Bola Tinubu, wallahi idan ya karbi mulkin kasar nan duk sai munyi dana-sani. Idan kuma kun ce karya ne, to kuyi sakacin bashi mulki ku gani!
Wannan shine gaskiyar magana. Kuma nasan wannan magana ba zata yiwa wasu makwadaita, karnukan farautar Bola Tinubu dadi ba. To ni dai wallahi babu ruwana, in dai har al’ummata sun fahimci gaskiya, kuma sun bi ta.
Kuma lallai ne mu sani, wallahi ya zama tilas, kuma wajibi, Gwamnonin mu, da dukkan ‘yan siyasar mu na arewa, da dukkan manyan mu, su hada kan su, domin su ciyar da yankin gaba. Idan ba haka ba kuwa, wallahi sai ‘ya ‘yan su da jikokinsu sun tsine masu albarka!
Ku duba ku gani, yadda Gwamnonin kudu maso yammacin Najeriya, wato yankin yarbawa, suka kafa wata runduna ta musamman, domin tabbatar da tsaro da ci gaban yankin su, mai suna Amotekun. Su ma Gwamnonin kudu maso gabashin Najeriya, wato yankin inyamurai, kwanan nan, sun ƙaddamar da runduna ta musamman da za ta rinka bai wa yankunan su tsaro mai suna Ebube Agu. Sun kuma jaddada cewa har yanzu haramcin da suka sanya na hana ‘yan uwan mu fulani kiwo a yankunan su, yana nan.
Sannan ‘yan yankin kudu-maso-kudu (South-South), su ma suna da ire-iren wadannan rundunoni. Amma abun mamaki, abun bakin ciki, yankin arewa ne kadai, zaka tarar da cewa Gwamnonin mu, sun ma kasa hada kai, bare su samar da irin wadannan rundunoni da zasu taimaka muna, wurin samar da tsaro! Allah ya sawwake, amin.
Kuma ina rokon masu arzikin mu, da ‘yan siyasar mu, da shugabannin mu, don Allah, don Allah, don Allah, su rinka taimaka wa talakawa, domin wannan zai taimaka, kuma zai rage masu radadin talauci, ya zama ko da wani yazo daga wani yanki da wata mummunar manufa, ko domin ya saye imanin su da kudi ko da abinci, to ba zai yi nasara ba. Amma idan kuna barin su cikin kuncin talauci da damuwa, babu taimako, to wallahi duk wanda yazo daga wani yanki, zai iya sa suyi masa duk abunda yake so, ko da kuwa abun marar kyau ne! Allah yasa mu dace, amin.
Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau ne ya rubuta, daga Okene Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.