Jam’iyyar PDP ta nemi a gaggauta cire Ministan Sadarwa da Bunkasa Fasashar Zamani, Isa Pantami, bisa furucin nuna goyon bayan kungiyoyin Alkaida da Taliban da ya taba yi can a baya.
An bayyana wani adiyo mai dauke da muryar Pantami ya na nuna goyon bayan Alkaida da Taliban, wanda ya jawo cece-ku-ce a kasar nan, har ana neman a tsige shi.
Pantami ya yi ikirarin cewa ya yi furucin a baya, amma daga baya kuma yanzu ya fahimci ba haka yadda ya yi tunani lamarin ya ke ba. Ya ce a yanzu ya canja fahimtar sa.
Tun cikin wata tattaunawa da ya yi da PREMIUM TIMES dai Pantami ya bayyana cewa ba shi da wata alaka ko kusanci da Boko Haram, Alkaida ko Taliban.
Ya shaida cewa wasu gaggan masu laifi ne ke kokarin kulla masa sharri, saboda ba su kaunar aikin hada lambar katin shaidar dan kasa da lambobin waya da ya ke yi.
Sai dai kuma wadannan karin haske da ya yi, bai hana jama’a da dama fitowa su nemi a kore shi a cire shi daga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ba.
Ranar Lahadi ma jam’iyyar PDP ta nemi a cire shi, bisa wadancan furuci da ya yi a baya.
“Mun damu matuka a matsayin mu, ganin cewa wannan minista da ake magana a kan sa, ya na rike da muhimmin mukamin dukkan bayanan kowane dan Najeriya babba da kanana, har ma da shugabanni da shugabannin bangarorin addinai” In ji Kakakin Yada Labarai na PDP, Kola Ologbondiyan.
PDP ta kuma nemi jami’an SSS su binciki Pantami, saboda “yadda ya bada kai bori yah au wajen yi wa bakin-haure daga kasashen waje rajistar katin dan kasa, a matsayin su ma ‘yan kasa ne.”
Tsakanin Pantami Da PDP:
Minista Isa Pantami ya shiga ‘yar tsama da PDP, tun kafin zaben 20215 wanda ya samu mukami bayan Buhari da APC sun yi nasara.
An rika watsa wani faifan bdiyo, inda aka nuno Pantami a masallaci ya na tsine wa jam’iyar PDP a lokacin da masallacin ke cike dankam da jama’a, ya na cewa:
“Allah ya karya jam’iyyar PDP kafira.”
Sannan kuma a lokacin da ake kashe-kashe a zamanin mulkin PDP, ya rika nuna tausayin wadanda ake kashewa har ya na kuka.