Pantami ya yi abin da ba a taba yi ba a kasar nan, zagon kasa ake yi masa – Fadar Shugaban Kasa

0

Fadar shugaban kasa ta ce tana tare da ministan Sadarwa, Ali Pantami Dari bisa Dari domin ya yi abinda ba ta taba yi ba a kasar nan.

A wata sanarwa da kakakin fadar shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar ranar Alhamis, gwamnati ba za ta lamunta wa duk wanda ya nemi ya tozarta minista Pantami ba saboda irin kokarin aiki da ya ke yi domin ci gaban kasa.

Shehu ya ce gwamnati za ta yi bincike akan abinda ake zargi akai da kuma bita-da-kullen da ake yi wa ministan game da ayyukan da ya saka a gaba na ci gaban kasa.

” Duk wanda aka samu da hannu yana kawo cikas a ayyukan da ake yi, zai fuskanshi fushin gwamnati.

” Eh, minista Pantami ya yi wasu maganganu a baya a wasu wa’azuzzukan shi, wanda ya ce wadannan matsaya da ya dauka sun canja yanzu. Wadannan duk basu shafi aikin sa ba. Maimakon a duba a gani ko a aikin sa ne ya ke samun matsala sai wasu mara sa kishi suka koma suna dauko wani abu daban duna yadawa don son zuciya irin ta su.

” Mun sani kuma munji daga bakunan wasu jaridun kasarnan da ke da kima wanda kuma suka san aikin su, ana ta kokarin basu toshiyar baki domin su ci mutuncin Pantami karfi da ya ji, amma suka kai karba.

” A karon farko a kasar nan, ma’aikatar sadarwa na kawo wa kasa kudaden shiga wanda ba ataba samun haka ba. Baya ga mai, ma’aikatar na sama wa kasa kudaden shiga fiye da kowacce ma’aikata a kasar nan. Sannan kuma Pantami ya kawo sauye-sauye na ci gaba wandanda basu misiltuwa.

A karshe Shehu ya ce lallai gwamnati ba za ta bar wannan magani ta wuce ba tare da an gudanar da bincike ba, kuma duk wanda aka samu yana da hannu zai dandana kudar sa.

Share.

game da Author