Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya na Landan ne ya na dan hutun kailula.
Haka dai Buhari ya fassara tafiyar da ya yi zuwa Landan domin ganin likita.
Cikin wata wasika da Buhari ya aika wa Shugaban Kasar Jordan, wadda Garba Shehu ya sanya wa hannu, wasikar ta bayyana cewa Buhari ya je hutu ne, ba ta bayyana cewa ba shi da lafiya ko ya je ganin likita ba.
Sanarwar da Fadar Shugaban Kasa ta bayar kafin tafiya da Buhari ya yi, ta ce zai yi makonni biyu a Landan sannan ya dawo gida.
Tafiyar ta sa ta hadu da bacin ran ‘yan Najeriya, wadanda su ke rika nuna fushin yadda Buhari ya tsallake ya bar kasar nan, a lokacin da likitocin kasar su ka shiga yajin aikin neman a biya su hakkokin su da gwamnati ta ki biyan su.
Bayan Buhari ya sauka Ingila dai ya hadu da fushin wasu gungun ‘yan Najeriya mazauna can, domin kuwa sun shafe kwanaki biyu su na zanga-kofar gidan Najeriya, inda su ka nemi ya koma Najeriya ya nemi magani kuma ya gyara asibitocin Najeriya.
Sannan kuma kwana biyu bayan tafiyar sa, ma’aikatan kotunan shari’a na kasar baki daya su ka kulle tun daga kananan kotuna har zuwa Kotun Koli, su ka tafi yajin aiki.
Wasikar ta Garba Shehu mai cike da godiya ga Sarkin Jordan Abdullah II Bin Al-Hussein, wanda tsaron Daular Bani Hashim ne, an kuma sanar da shi cewa an taya shi murna da jinjina masa bisa matsayar da aka cimma wajen dakile barakar da ta kunno kai cikin fadar masarautar ta Jordan.
Buhari ya bayyana cewa ran sa ya baki jin cewa an samu baraka cikin gidan sarautar Jordan. Amma kuma ran sa ya yi fari jin cewa an dinke barakar.
Discussion about this post