Najeriya ta nemi sulhu da Boko Haram, a daina kashe naira tiriliyan 1.2 duk shekara kan yaki da ta’addanci – Tsohon Jakadan Aljeriya

0

Wani masanin huldar diflomasiyya, kuma tsohon Jakadan Najeriya a kasar Algeria, ya bayyana cewa zai fi zama alfanu ga tattalin arzikin Najeriya, idan aka yi sulhu da Boko Haram, su daina kisa da ta’addanci a Najeriya, domin kasar nan ta daina ragargaje sama da naira tiriliyan 1.2 duk kowace shekara da sunan kudin yaki da Boko Haram.

A wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a ranar Litinin a Abuja, Nnamdi Onochie ya jaddada cewa irin makudan kudaden da Najeriya ke narkaswa da sunan yaki da Boko Haram, hakan na yi wa tattalin arzikin kasar nan mummunar illa.

Onochie wanda aka tattauna da shi dangane da kisan Shugaban Chadi Idriss Deby, ya ce mutuwar Deby babbar barazana ce ga tsaron Najeriya.

“Yanzu Chadi ta afka sabon rikici tun bayan mutuwar Deby. Wannan rikici zai iya shafar Najeriya a kokarin da kasar nan ke yi ta kawo karshen ta’addanci.

“Sabo da haka ina ba Najeriya shawara cewa kada ta kuskura ta tsoma baki ko tsoma kafa a rikicin cikin gida na Chadi.

“In da a ce zan zama Shugaban Kasa a 2023, to zan nemi sulhu da Boko Haram, domin a kawo karshen kisan jama’a barkatai da ake yi dubbai a kasar nan. Sannan kuma za a kawo karshen asarar naira tiriliyan 1.2 da ake yi da sunan yaki da Boko Haram.

Sai dai kuma tsohon jakadan ya kasa yin bayanin cewa Boko Haram akida ta masu hankoron kafa daular musulunci, ba sasantawa ce gaban su ba.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda fiye da Boko Haram 4,000 su ka zubar da makaman su.

Sama da ‘yan Boko Haram 4,000 ne su ka zubar da makaman su, su ka bar sansanonin ta’addanci a kasashen Najeriya, Chadi, Nijar da Kamaru.

Wani rahoto ne ya tabbatar da haka, wanda Kungiyar Bin Diddigin Matsalar Tsaro a Afrika, mai suna ISS ta fitar kwanan nan.

Wannan adadi ya nuna an samu matukar raguwar manyan kwamandoji da sauran karabitin mayakan Boko Haram a cikin kasashen hudu.

Rahoton wanda ISS ta fitar ya na kunshe ne a cikin shafuka 28, wanda ya bayyana cewa ‘yan Boko Haram sama da 2400 su ka zubar da makamai a Chadi, 1000 a Najeriya, 584 a Kamaru, sai kuma 243 a Nijar.

ISS ta bayyana cewa dalilai da yawa ne su ka sa masu ta’addancin har sama da 4,000 su ka watsar da makaman na su.

Dalilan sun hada cewa, wasu ‘yan Boko Haram din ba don akida su ka shiga ba, kama su aka yi da karfin tsiya aka saka su cikin ta’addanci, bayan an yi garkuwa da su.

Sannan kuma akwai dalili na matsin lambar da su ke fuskanta, saboda yawan hare-haren da sojojin hadin-guiwa na MJTF ke kai masu a Yankin Tafkin Chadi.

Wannan ya sa rayuwar su ta shiga cikin hatsari, babu sakewa ko kadan.

Da yawan wadanda su ka shiga domin akida sun dawo daga mummunar akidar, sun gane ba tafarkin tsira ba ne.

Rahoton ya nuna akwai tsatstsauran hukunci ga masu karya doka a cikin sansanonin Boko Haram. Fasikanci da sata abu ne mai gamuwa da kakkarfan hukuncin da ke kara tsoratar da wasu da dama, musamman ganin yadda ake aiwatar da hukuncin.

Sannan kuma akwai rashin jituwa da kuma adawa tsakanin bangarorin masu ta’addanci. Sai kuma dalilan saduda da daidaikun ‘yan ta’adda ke yi, su na gajiya da kasancewa cikin rayuwar kunci a cikin dazuka.

Wata Jami’ar Bincike a ISS mai suna Teniola Tayo, ta bayyana cewa adadin gaskiya ne, kuma gwamnatocin kasashen hudu sun yi na’am da rahoton.

Shi ma Malik Samuel na ISS ya bayyana cewa ba shaci-fadi su ka yi wajen tattara adadin har na sama da Boko Haram 4,000 ba.

“A Najeriya mun samu adadin ne da ‘Operation Safe Heaven’, cibiyar ta ke kula da tubabbun ‘yan Boko Haram da kuma yi masu wankin kwakwalar kankare masu akidar ta’addanci.

Share.

game da Author