NAJERIYA CIKIN WATANNI UKU: Hatsarin mota 2,690 ya ci rayuka 1,302, wasu mutum 8,141 sun ji raunuka

0

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) ta bayyana cewa a cikin watanni uku da su ka gabata, an samu salwantar rayukan mutum 1,302 sanadiyyar hatsarin mota a Najeriya.

A cikin wata tattaunawa da Babban Jami’in Wayar da kan Jama’a na FRSC, Bisi Kazeem, ya bayyana cewa sun tattara bayanan adadin hatsarin motoci har sau 2,690 a Najeriya.

Ya kuma kara da cewa baya ga rayukan mutum 1,302 da aka rasa, mutum 8,141 ne su ka ji ciwo. Sannan kuma an ceto kimanin mutane 8,302.

Kazeem ya yi karin hasken cewa dalilai da yawa ne ke haddasa yawan afkuwar hadurra kan titinan Najeriya.

“Ka ga dai akwai halayyar wasu direbobin, rashin lafiyar mota, rashin kyan titina, gudun-wuce-sa’a da sauran dalilan da su ka danganci karya dokokin tuki.”

Kazeem ya ce a kowane lokaci Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa na bakin kokarin ganin masu motoci na bin dokokin tuki a kan titina.

Sanann kuma ya ce hukumar na bakin kokarin ta wajen wayar wa masu ababen hawa kai dangane da muhimmancin bin ka’idojin tuki da kuma hatsarin da a kan iya riska idan ana tuki ba tare da kiyayewa da bin ka’idojin ba.

Wannan adadin rayukan da su ka salwanta har 1,302, an bayyana shi kwana daya bayan fito da adadin kisan mutum 239 da aka yi kasar nan a hare-haren tashe-tashen hankula cikin mako daya da ya gabata.

Share.

game da Author