Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) Reshen Jihar Kano, ta bada sanarwar damke wasu masu safarar kayan sinadaran kara wa ruwan lemuka zaki, da aka fi sani da danzaki, bayan da wasu mutum uku su ka mutu sanadiyyar shan sinadaran.
NAFDAC dai ta yi gargadin cewa sinadaran gurbatattu ne, kamar yadda Shugabar Hukumar NAFDAC ta Kasa, Mojisola Adeyeye ta sanar a cikin wata takarda da jami’an tuntuba na NAFDAC, Olusayo Akintola ya fitar a ranar Lahadi, a Abuja.
Daga nan ta yi gargadin cewa a guji irin wadannan sinadarai, domin shan sun a yi wa mutum mummunar illar da ke iya kaiwa ga kisa.
Adeyeye ta ce babu wani da zai iya taka wa NAFDAC burgi a kokarin da hukumar ke yi wajen ganin ta tsaftace duk wani abinci da abin sha a fadin kasar nan, domin kare lafiya da rayukan jama’a.
Sannan kuma ta bayyana cewa ta mika wa Gwamnan Kano Umar Ganduje sakamakon binciken farko da hukumar ta fitar a ziyarar da ta kai Kano domin gane wa idon ta lamarin da ya faru a birnin na Kano.
Ta nuna rashin jin dadin yadda wasu marasa imani ke shigo da kayan da gurbatacci ne daga kasashen waje, domin kawai su samu mummunar riba a kasuwancin su, amma babu ruwan su da yawan jama’ar da su sallwanta ko za su jikkata.
Adeyeye ta kara da cewa ana samun gurbataccen abinci ko abin sha ta hanyar amfani da wanda lokacin amfani da su ya wuce, ko wanda aka hada da gurbataccen ruwa ko gurbataccen sinadari, ko kuma wanda ya dade ajiye a kan kanta a cikin shaguna ko kantina.
Ta yi hani da rika kara wa ruwa ko abinci wani sinadarin da zai kara masa dadi ko zaki.
Discussion about this post