A dalilin dakatar da yarjejeniyar dake tsakanin kamfanin MTN da bankunan kasar nan, wanda ya sa bankuna suka dakatar da Kamfanin sadarwar da ga ci gaba da amfani da su wajen siyar wa masu amfani da layukan MTN katin kira.
MTN ya bayyana wasu sabbin kafofi da hanyoyin da masu amfani da layukan su za su iya siyan katin kira ba sai dole sun siya ta asusun ajiyar su na banki ba.
Hanyoyin kuwa sun hada da:
1. MTN On Demand is on *904# and also via https://mtnondemand.flutterwave.com;
2. Barter By Flutter Wave is an app that can be downloaded here: http://tosto.re/getbarter;
3. Jumia Pay (app);
4. OPay (app);
5. MTN Xtratime airtime loans (*606#);
6. Carbon (app);
7. Kuda (app);
8. BillsnPay (web https://www.billsnpay.com/. They also have an app);
9. myMTN Web http://mymtn.com.ng;
10. Momo agent *223#
MTN ya ce za a iya sauke wasu daga cikin manhajar daga Google Play Store. Duk wanda ka bi za ka siya katin kira babu matsala.
Sai dai kuma ministan Sadarwa, Ali Pantami, ya bayyana cewa ya shiga tsakanin bankuna da MTN domin a samu matsaya daya game da sabanin da ke tsakanin su, kuma an samu nasara a zaman farko da aka yi.
Idan ba a manta ba ‘Yan Najeriya sun fada cikin halin kakanikayi da gararamba bayan bankunan Najeriya sun dakatar duk wani mai layin MTN iya siyan katin kira ta asusun ajiyar sa na banki tun daga ranar Alhamis.
Bayan mutane sun kasa iya siyan katin kira ta bankunan su aka fara korafi da neman bayanai daga bankunan da kamfanin sadarwar MTN. MTN ta aika wa masu amfani da layin kiran cewa daga yanzu duk mai son kira da layin MTN ya garzaya shagunan siyar da kati kai tsaye da kuma irin na bakin hanya ya kai tsaye.
PREMIUM TIMES ta gano cewa an samu tankiya ne a tsakanin MTN da bankuna wurin raba ribar kudaden da ake cirewa idan aka siya katin.