Makonni biyu kenan bayan wasu kungiyoyi sun ja hankalin Ministan Sadarwa Isa Pantami dangane da wasu jami’an Hukumar Sadarwa ta Kasa, wadanda su ka yi zambar naira miliyan 122, har yau Minista Pantami bai dauki matakin koma ba a kan su.
Duk da cewa Hukumar Sadarwa ta Kasa, NCC ta furta cewa tabbas jami’an na ta biyu sun saci kudaden har naira miliyan 122, har yanzu kuma ta ki tabbatar da cewa an hukunta jami’an da su ka dibga satar kudaden.
Cikin watan Maris ne PREMIUM TIMES ta ruwaito yaddda manyan Jami’an Hukumar Sadarwa ta Kasa su biyu, Yakubu Gontor da Philip Eretan su ka karbi kudaden alawus din tafiye-tafyen da ko ko filin tashin jirage bas u je ba, ballantana su yi tafiye-tafiyen da su ka karbi kudaden don su yi.
Dan dankara wa Gontor naira miliyan 54, shi kuma Eretan ya kamfaci naira miliyan 68 ya zuba aljihu, ya yi mirsisi abin sa.
Cikin shekarar 2020 ne dai wani kwamitin binciken da aka kafa ya kama su da laifi, amma har yau ba a gurfanar da su kotu ba.
PREMIUM TIMES ta gano cewa ana ci gaba da cire kudaden da su ka sata daga cikin albashi da alawus din mazambatan su biyu, amma dai an ki kai su kotu ballantana a hukunta su kamar yadda dokar aikin gwamnatin tarayya ta gindaya.
Sai dai kuma PREMIUM TIMES ta gano cewa Hukumar NCC a karkashin shugaban ta Umar Dambatta, ta yi mirsisi, ta kauda kai daga gurfanar da su a kotu.
Kada a matana NCC ta karbi lambar yabo daga ICPC dangane da sharafin da hukumar ta yi wajen bin ka’idar iya aiki. Amma duk wa wannan hukumar ta kauda kai daga wadannan ma’aikatan ta biyu mazambata.
Ita dai Hukumar NCC, hukuma ce da ke karkashin Ministan Sadarwa Isa Pantami.
Amma kuma PREMIUM TIMES ta gano cewa jami’an na NCC biyu da su ka jidi naira miliyan 122, sun rika jekala-jekalar zuwa ofishin EFCC da ke kaduna, tsakanin watan Fabrairu da Maris.
Sai dai kuma sabbin shugabannin EFCC sun shaida wa Premium Times sun kasa gano inda bayanan wannan batun satar kudade su ke.
Cikin Fabrairu, sabon Shugaban EFCC na shiyyar Kaduna, Sanusi Abdullahi, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa cikin watan Yuli, 2020 aka yi masa canjin wurin aiki zuwa Shiyya. Kuma ya kasa gao inda kwafe-kwafen bayanan harkallar satar wadannan makudan kudade ku ke.
Duk da haka ya ce za su ci gaba da bincike.