Kungiyar Kwallon Kafa ta Liverpool sun yi tofin Allah-wadai ga wasu takadaran magoya bayan su, dangane da farfasa gilasan motar da aka dauki ‘yan wasan Real Madrid da ita.
Takadaran sun kai wa motar hari ne a lokacin da ta ke shiga a harabar filin wasan Liverpool, kafin a fara wasan da aka tashi kunnnen-doki tsakanin kungiyoyin biyu a jiya Laraba, a birnin Liverpool da ke Ingila.
Harin da aka kai wa motar ya janyo an farfasa gilasan tagogin motar. Sannan kuma an ruwaito cewa wasu mafusatan magoyan bayan Manchester City sun kai wa motar da ta dauki ‘yan wasan Real Madrid farmaki.
Wadanda lamarin ya faru kan idon su, sun hakkake cewa an kuma kai wa kociyan Real Madrid hari inda aka rika jifar motar da ya ke ciki a bangaren sa.
Mahukuntan kungiyar Liverpool sun bada hakuri tare da daukar alkawarin sai sun gano wadanda su ka kai harin, kuma sai an hukunta su.
Ba a dai san wani takamaimen kai wa motar hari ba, amma ana tunanin haushin fitar da Liverpool a wasan karshe na Champions League din 2018 ne ya sa aka kai wa motar hari.
“Mu na bai wa Real Madrid hakuri tare da yin tir da wannan abin takaici na harin da ya faru a kan motar daukar su a daidai lokacin da motar ke isa da su a filin Anfield da daren nan.”
Haka kakakin yada labarai na iverpool ya bayyana.
“Ba za mu taba yarda, amincewa ko goyon bayan wata ko wani mugun halin wasu takadarai ba da sunan magoya bayan kungiyar Liverpool.
“Mu na bada hakuri ga manyan bakin mu dangane da duk wani takaici da wannan hari zai haifar masu. Kuma za mu yi aiki tare da ‘yan sandan Merseyside domin tabbatar da an damke dukkan wadanda su ka kai wannan hari, marasa mutuncin banza.”
Haka ta taba faruwa, inda a wasan kwata-fanal da Manchester City, a 2018 aka kai wa motar su hari a filin wasa na Liverpool.
Da dama na ganin cewa Hukumar Kwallon Kafa ta Turai, UEFA za ta yi wa Liverpool tsatstsauran hukunci, ganin cewa wannan shi ne karo na biyu da ake kai wa wasu ‘yan wasa hari ta hanyar jifar motar su da duwatsu.