MATSALAR TSARO: Najeriya ba ta afkawa cikin irin wannan mawuyacin halin a baya ba – Minista Akpabio

0

Ministan Harkokin Bunkasa Yankin Neja Delta, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa Najeriya ba ta taba samun kan ta mawuyacin halin da ta tsinci kan ta ba a yanzu.

Akpabio ya kara da cewa ya tabbata wadannan tashe-tashen hankula akwai batutuwa na siyasa a tare da su.

” Ina ganin matsalolin da su ka afka wa kasar nan a yanzu akwai siyasa a ciki. Saboda ba mu taba shiga irin wannan mawuyacin halin ba.

“A karon farko an wayi gari ga Boko Haram, ga ‘yan bindiga da barayin dukiyoyin jama’a. Sannan kuma ga masu garkuwa da mutane ba ji ba gani.

“Sannan kuma an wayi gari wasu sun bayyana wadanda ta su barnar ita ce kai wa jami’an tsaro hare-hare su na kashe su. Gaskiya ba mu san da haka ba a baya.

“Ya kamata mu koma daga tushe mu yi amfani da yaru kan mu na haihuwa, mu zakulo tare da fallasa wadannan mugayen mutane masu kokarin kassara Najeriya.”

Akpabio na ganin cewa lamarin nan akwai sa hannun bakin-haure a tashe-tashen hankulan kasar nan.

Da ya ke magana bayan taron masu ruwa da tsaki na APC, Akpabio ya ce ya yi amanna da shugabancin rikon da Gwamnna Mai Mala ke wa APC.

Share.

game da Author