MATSALAR TSARO: Abinda Gumi da tawagarsa suka tattauna da Obasanjo a Abeokuta

0

Wata tawagar wasu dattijan Arewa karkashin jagorancin Sheikh Ahmed Gummi sun kai wa Tsohon Shugaban Kasa, Ousegun Obasanjo ziyara, a kokarin su na neman mafita daga matsalar tsaro, musamman garkuwa da mutane, samamen kona kauyuka da kuma kawo karshen biyan diyyar wadanda ake yin garkuwa da su.

A tawagar Gumi akwai Usman Yusuf, Tukur Mamu, Umar Ardo, Ibrahim Abdullahi Suleiman Gumi, Suleiman Yakubu da Buba Mohammed. Duk sun dunguma zuwa gidan Obasanjo da ke Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.

Taron na su ya maida hankali ne kacokan a kan musabbabin hare-haren ‘yan bindiga da garkuwa da mutane. Sai kuma matsalolin da rashin tsaro ya haifar a cikin al’umma, da kuma yadda sauran jama’a su ka dauki mataki a yankunan kasar nan da ma wasu kasashen Afrika ta Yamma.

Gumi ya bayyana wa Oabsanjo irin matakan da ya dauka wajen ganin an magance matsalar garkuwa da mutane, hare-hare da kashe-kashen ‘yan bindiga da biyan diyya a sassa daban-daban na Arewa.

Bayan kammala taron, Obasanjo da Gumi sun sa wa takardar bayan taro hannu, wadda a ciki su ka fitar da shawarwarin cewa sun amince su ci gaba tuntubar juna domin samar da mafita daga kangin matsalolin tsaro a Najeriya.

Cikin sanarwar da su ka fitar, sun kuma yi kira ga sauran jama’a masu kishi su shigo cikin su domin a rungumi matsalolin hannu bib-biyu yadda za a yi wa kalubalen taron dangi.

“A kan haka, Gumi ya gayyaci Obasanjo ya je Kaduna domin ci gaba da wannan muhimmiyar tattaunawar da su ka fara. Kuma Obasanjo din ya amince cewa zai kai ziyarar Kaduna.” Haka sanarwar ta bayyana.

Taron ya bayyana cewa sun gano wasu dalilan da ke haddasa rikici tsakanin Fulani makiyaya da sauran mazauna yankunan da Fulanin su ke zaune. Kuma sun nemi jama’a su sa hannu wajen ganin an shawo kan wannan matsala.

Takardar bayan taron ta kuma yi kira da aka rika mutunta juna tsakanin kalibu da kuma sauran kabilun da ke cudanya da juna kozaune da juna ko makawautaka da juna.

Taron ya kuma ce ya kamata jihohi su kasance su na da iko da karfin iya magance matsalolin da ke addabar yankunan karkara. Haka ita ma gwamnatin tarayya ya kasance ta na samar da hanyoyin hana faruwar wata matsala, maimakon a bari sai matsala ta faru sannan a rika gaganiyar neman ruwan yayyafawa don a kashe ta.

“Gwamnatin Tarayya ta gaggauta samar da shirin maida yaran da ke gararamba zuwa makarantu domin su samu ilmi. Kuma jama’a su rika fallasa masu dauke da makamai.

“Sannan kuma a baro wadanda su ka amince za su ajiye makamai daga cikin daji. A tsugunar da su, a koya masu sana’o’in hannu kuma a ba su jarin samun sana’a. Su kuma wadanda su ka ki mika wuya, sai a kwankwatse su kawai.”

A karshe takardar bayan taron ta yi kira ga kasashen da ke karkashin Kungiyar ECOWAS su zauna su hada kai wajen dakile safarar makamai tsakanin kasashen da kuma samar da hanyoyin dakile rikice-rikicen da al’ummomin yankunan kasashen ke sfama da su.

Share.

game da Author