Bayan samun nasarar kara sabbin dandanon Abarba da Vanilla cikin jerin kayan sha da Kamfanin Maltina ke sarrafawa wanda ita ce kan gaba wajen sarrafa kayan sha da ake yi da sanadarin Malt, ta kaddamar da sabbin dandanon Abarba da Vanilla a Kano.
An yi bikin kaddamar da wadannan kayan sha masu dandanon Abarba da Vanilla a ginin Ado Bayero Mall dake Kano ranar 11 ga Afirilun 2021.
A wannan rana da aka kaddamar da wadannan kayan sha na Maltina masu dandanon Abarba da Vanilla, mutane sun yi tururuwa zuwa wannan dandali in da aka nishadantar da kayatar da su da wasanni dabam dabam domin jin dadin su.
Yaran makaranta ma ba a barsu a baya ba. Sun wataya tare da iyayensu da abokanan su kuma sun rika kwankwadar wadannan sabbin dandano na Maltina, wato dandanon Abarba da Vanilla a lokacin da suke watayawa.
Bayan haka an gudanar da wasanni domin su kuma sun fafata a tsaninsu. Wadanda suka yi nasara an raba musu kyaututtuka masu dauke da tambarin Maltina daga kamfanin.
Su ma iyayen yaran ba a barsu a baya ba, an gudanar da gasa da ya kunshi tambayoyin wasa kwakwalwa. Wadanda suka yi nasara an raba musu kyaututtuka.
Iyaye da ya’yan su sun bayyana farin ciki kakara, sannan an rarraba musu kyaututtukan kayan sha na gora da gwangwani na Maltina su tafi da su gida su kuma rarraba a tsakanin su. Bayan haka sun godewa kamfanin Maltina kan wadannan kyaututtuka da suka raba musu a dalilin wannan biki.
Daya daga cikin kololowar abinda ya auku shine bayyanar jarumar fina-finan Hausa na Kannywood Rahama Sadau a wajen bikin, wanda Jakadiyar Maltina ce.
Babban manaja a Kamfanin Maltina Elohor Olumide-Awe ne ta shigo da Sadau wannan wuri inda gaba daya wurin taro ya cika da murna ganin jarumar ta shigo.
A jawabinta, Rahama Sadau ta jinjina wa kamfanin Maltina da ma’aikatanta sannan ta godewa Kamfanin da ta kaddamar da wadannan dandano biyu a garin Kano.
A jawabin ta shima, babban manaja a kamfanin, Elohor Olumide-Awe ta bayyana cewa an shirya wannan kasaitaccen biki ne domin taya ‘yan Najeriya murnar kammala bukukuwan Easter da fara azumin watan Ramadan.
” Shekara 45 kenan da Kamfanin Maltina ta kirkiro’ Maltina Classic’ a kasuwannin Najeriya. A wannan lokaci ne muka ga ya fi da cewa mu fidda wadannan sabbin dandano na Vanilla da Abarba kuma a jihar Kano.
” Sakon mu na musamman daga kamfanin Maltina shine, a rika yada farinciki ta kowani hanya wanda hakan yasa muke sanar da haka ga dukka abokan huldan mu a nan Kano suma su rika yada wannan manufa ta mu na farinciki a koda yaushe tare da abokanan arziki musamman a wannan lokaci na azumin watan Ramadana.
Bayan an wataya an nishadantu da wasanni, da shirye-shirye na barkwanci da wakoki, wannan taro ya burge mutanen Kano matuka.
Game da Maltina
Kamfanin ‘Nigerian Breweries PLC’ , ne ke sarrafa Maltina wanda aka fara yin sa a Najeriya tun a 1976.
Maltina na kunshe da sinadarin Vitamin A, B1, B2, B3, B5, B6 da Calcium da ya sa Maltina ya zamo abin sha mai amfani ga dukkan iyali.
Yana da dadin sha da gamsarwa kuma kowa zai ji dadin shan sa a ko da yaushe a kuma kowani lokaci.