MAKON RUBDUGUN KISAN ‘Yan Najeriya: An kashe mutum 239, an sace mutum 44 a makon jiya

0

Halin da talakawa su ka shiga a makon da ya gabata a sassa daban-daban na kasar nan, ya kara nuna ci gaba da kasawar Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’ar kasar nan.

Munin kashe-kashen makon da ya gabata ne ya kai ga Wole Soyinka fitowa ya bayyana cewa Najeriya fa ta rufta yanayin yakin ‘katilan-makatulan’, amma gwamnati ta kauda kai ba ta yarda yaki ne ake yi gaba-gadi ba.

Cikin makon da ya gabata kididdigar labarai ta bayyana cewa an kashe akasarin talakawa 239 kuma aka yi garkuwa da mutum 44 duk a cikin mako daya.

Yayin da a Jihar Zamfara aka kashe mutanen karkara sama da 90 a hare-hare daban-daban a Magami da kewaye, cikin Karamar Hukumar Gusau, a Jihar Yobe Boko Haram sun yi dirar mikiya a Geidam, garin haihuwar sabon Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Usman Alkali.

A jihar Oyo kuma ‘yan bindiga ne su ka tare hanya su ka yi gaskuwa da dukkan fasinjoji 18 da ke cikin wata motar haya.

Matsalar tsaro ta kai ga an kai hari da rokoki a gidan Gwamnan Imo Hope Uzodinma, kamar yadda a baya aka taba kai wa jerin gwanon motocin Samuel Ortom na Benuwai hari a cikin daji.

Irin haka ta faru da Gwamna Babagana Zulum na Barno, ba sau daya ba an kai masa hari.

A jihar Katsina ma mahara sun yi garkuwa da mata su 20 da su ka halarci bikin radin suna.

Haka a jihar Kaduna ‘yan bindiga sun saci daliban jami’ar Greenfield University, kuma su ka kashe uku daga cikin su.

Matsalar tsaron da ke ci gaba da faruwa ta nuna canja manyan hafsoshin tsaro da kuma canja Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, duk an ki cin biri ne, an ci dila.

Share.

game da Author