Wasu sanatoci a majalisar dattawa sun bayyana cewa maimakon su zauna a majalisar suna ta surutu amma kuma a waje ana ta kashe ‘yan Najeriya.
Sanata Ike Ekweremadu, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawa ya ce baiga amfanin ci gaba da zama a majalisar ba, kisan yayi yawa sannan kuma gwamnatin tarayya ta gaza yin komai akwai.
Duk gwamnatin da ba ta iya samarwa mutanen kasarta tsaro ba to lallai wannan gwamnati ta gaza.
Sanata Smart Adeyemi, wanda ya barke da kuka a lokacin da yake jawabi, ya yi kira ga sanatocin da su cire siyasa kowa ya tattaro hankalin sa wuri daya a sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari halin da kasa ke ciki.
” Gaskiyar magana shine Najeriya ta shiga halin kakanikayi game da matsalar rashin tsaro wanda bata taba fadawa ciki ba. Wannan matsala fa ya kai intaha, dole mu ajiye siyasa a gefe mu fada wa kan mu gaskiya. Ko ina ya dagule, babu tsaro.
” Yau mutum bashi da damar yin tafiya a Najeriya, ko ina ana cikin matsala na tsaro. Ina zamu saka kan mu. Abu ya kai ga hatta ana kakkafa tutoci a wasu ya kunan kasar nan.
Sanata Adeyemi Smart, a karshe dai sai da ya barke da kuka, ya rika zubda hawaye kafin ya kammala jawabin sa.
Sannan kuma ya ce idan taimako ne Najeriya ke bukata, ta garzaya waje ta nemo mana.
Discussion about this post