Mahara sun bindige dan uwansu garin gudun tsira daga jami’an tsaro a Kaduna

0

Kwamishinan yada tsaron jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya bayyana cewa wasu mahara sun kashe dan uwansu wajen gudun tsira daga fafuran jami’an tsaro a karamar humumar Kajuru, jihar Kaduna.

Aruwan ya ce a bayanana abinda suka auku wanda rundunar yan sandan jihar Kaduna ta mika masa, mahara sun afka wani kauye mai suna Kajuru-Buda sai dai ba su yi nasara ba domin yan bindigan garin sun fatattake su.

Garin gudun tsira ne fa suna harbi ta ko-ina sai ko wano cikin su ya dirka wa dan uwansa harsashi, nan take ko ya sheka lahira.

Sai dai kuma kash, a karamar Giwa, wasu maharan sun kashe wani manomi Isah Haruna a gonar raken sa.

Haka kuma jami’an tsaro sun sanar da kashe wasu mazauna kauyen Wawan Rafi II dake karamar hukumar Zangon Kataf, jihar Kaduna.

An kai harin ne da sanyin safiyar litinin kafin wasu su farka daga barci.

Bayan mutum biyun da aka bayyana a baya, an samu karin wasu mutum biya da aka kashe sannan aka jefa cikin wani tafki. Syma an tsamo gawarwakin su, kamar yadda kwamishinan ya bayyana.

Share.

game da Author