Dukkan ma’aikatan kotunan Najeriya da ma’aikatan da ke ma’aikatar shari’a dake karkashin Kungiyar Ma’aikatun Kotuna da Bangaren Shari’a, sun bada sanarwar shekawa yajin aikin da sai hali, domin su matsa lambar a bai wa bangaren shari’a cin gashin kai.
Ma’aikatan a karkashin Kungiyar JUSUN, wato Judicial Staff Union of Nigeria, sun fitar da wata sanarwa a ranar 1 Ga Afrilu cewa kada su sake su bari a bude kowace kotu a fadin kasar nan daga ranar Talata, 6 Ga Afrilu, 2021.
Sanarwar wadda kwafen takardar ya fado hannun PREMIUM TIMES, kuma Babban Sakataren JUSUN I.M Adetola ya sa wa hannu, ya umarci dukkan rassan kungiyar na kowace jiha da shiyya su tabbatar da sun bi wannan umarni.
JUSUN ta ce tun a ranar 13 Ga Maris, bayan sun tashi taro a Abuja, sun bada wa’adin kwanaki 21 ga gwamnati ta fara aiki da tarin cin gashin kan bangaren shari’a.
JUSUN ta yi kurari da barazana a lokacin cewa idan gwamnati ba ta fara aiki da tsarin ba bayan cikar wa’adin da ta bayar, to ma’aikatan kotuna a fadin kasar nan za su sake komawa yajin aikin da su ka dakatar, wanda idan su ka koMa yajin aikin a yanzu, ba a san ranar komawar su aiki ba.
‘Mu Fito Mu Kulle Dukkan Kotunan Najeriya Da Ma’aikatun Shari’a’:
“Ana umartar duk wani ma’aikatacin kotu da ma’aikatan ofisoshin shari’a su fito a ranar Talata mai zuwa, su kulle dukkan kotunan kasar nan a jihohin da su ke, har sai sun ji wani umarni daga Babbar Hedikwatar JUSUN daga Abuja, kafin su bude.”
Wannan yajin aiki ya kara wa ‘yan Najeriya shiga halin matsin da su ka shiga, tun bayan fara yajin aikin da kungiyar likitoci ta NARD su ka fara, kwanaki biyu bayan tafiyar Shugaba Muhammadu Buhari zuwa Landan domin ya ga likitocin sa.
Discussion about this post