Jami’an Kiwon Lafiya masu aiki a karkashin Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC), sun bi sahun Kungiyar Likitocin Najeriya sun tafi yajin aiki.
Ma’aikatan wadanda su ma mambobi ne na Kungiyar Jami’an Kiwon Lafiya na Najeriya, sun bayyana cewa na su yajin aiki, na gargadi ne, wato kwanaki bakwai, domin su bayar da wa’adin biya masu bukatun su da kakkokin su cikin sati daya, ko kuma su tsunduma yajin aikin da babu ranar komawa bayan mako guda nan gaba.
Mataimakin Shugaban Kungiya mai suna Idzi Isua ya tabbatar wa PDEMIUM TIMES da tafiyar su yajin aikin, a wata tattaunawa da wannan jarida ta yi da shi a ranar Alhamis.
Daga cikin abinda ma’aikatan ke nema a biya su a matsayin hakkin su, akwai kudaden ariyas na shekarar 2018 da 2019 da su ka ce har yau gwamnatin Buhari ba ta biya su ba.
Kudaden dai sun wajaba a kan duk wanda aka yiwa karin matakin albashi, amma kuma a wadancan shekarun sai ya kasance duk da an kara masu matakin albashi na gaba, sai aka ki biyan su karin albashin da aka yi masu.
“Babban abin damuwar kuma shi ne, wadanda aka yi wa karin matakin albashi a shekarun 2018 da 2019 duk da an kara masu albashin, har yau ba a biya su ba. To yanzu kuma wadanda aka yi wa karin matakin albashi cikin 2020, za su shiga cikin irin matsalar da mu ka shiga kenan.” Inji Isua.
Sauran abubuwan da su k enema sun hada da gaggauta dawo da yi masu horo da kuma sanin makamar aiki.
“Saboda NAFDAC na fakewa da cutar korona ta na kin yi mana komai. Amma kuma sauran hukumomin Gwmnatin Tarayya tuni su key i wa ma’aikatan su horo da sanin makamar aiki.s