Ma’aikatan Hukumar FCT za su daina zuwa aiki saboda Ministan Abuja ya ‘rike masu wuya’

0

Hadaddiyar Kungiyar Ma’aikatan Gundumar FCT Abuja (JUAC), sun kammala shirye-shiryen tafiya yajin aiki, har sai an fara aiki da Dokar Tsarin Aikin Hukumar FCT tukunna.

Sun bayyana cewa za su tafi yajin aikin ne, saboda an ki yin amfani da dokar wadda za ta amfani ma’aikatan Hukumar FCT.

Shugaban Hadaddiyar Kungiyar, Matilukoro Korede, ya bayyana wa manema labarai a ranar Litinin cewa bai yiwuwa gwamanati ta dora kundin dokar FCT kan kanta ya na shan kura, alhali kuma ta ki fara amfani da dokokin ta yadda za su amfani ma’aikata, tunda dama makasudin kafa dokokin kenan, domin su amfani ma’aikatan.

Korede ya ya kara da cewa Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Muhammad Bello ne ya ki yarda ya fara aiki da dokokin, wadanda Shugaba Muhammdu Buhari ya sa wa hannu tun shekaru uku da su ka gabata.

Shugaban Kungiyar ta Ma’aikatan FCT ya kara da cewa, “Ministan Abuja ya cire masu tayoyi, ya dora su a kan turken jaki, tamkar ya maida kaddarar alherin da su ke jira ya same su a hannun sa, sai sadda ya ga dama zai saki.

“Mu kuwa mun gaji haka nan, daga wannan lokacin ba za mu sake saurara mas a ba, gara mu ma mu tafi yajin aiki, mu nuna masa iyakar sa.”

Ya kara da nanata cewa cikin makon da ya gabata su ka kammala yajin aikin gargadi na kwanaki uku, wanda shi ne alamar da ke nuna cewa sun gaji da yadda kakudubar siyasa ke shafar jin dadi da more rayuwar su a lokacin aiki, a matsayin su na ma’aikatan Hukumar FCT.

A kan haka ne ya ce Hadaddiyar Kungiyar Ma’aiakatan FCT da na FCDA sun shirya tafiyar yajin aikin da za a daina jin duriyar su.

Share.

game da Author