An so a tayar da jijiyoyin wuya a zaman Kwamitin Binciken Harkallar Kudaden Makamai na Majalisar Tarayya a ranar Litinin, yayin da Babban Hafsan Askarawan Najeriya, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru ya bayyana.
An nemi ya yi karin bayani, inda Attahiru ya bayyana cewa babu wani karin bayanin da zai yi, domin duk wata maganar da zai yi, ta na cikin kwafen daftarin kundin bayanan da ya damka wa kwamitin, wanda dama kuma shi aka ce ya gabatar wa kwamitin.
Attahiru ya jajairce cewa bai san komai dangane da batun kudaden makamai ba, domin ba a lokacin sa aka yi kwangillar cinikin makaman ba. Kowa ya san shi a kwanan nan aka nada shi.
“Ya kamata ku sani cewa ni Babban Hafsan Askarawan Najeriya ban fi watanni biyu da hawa kan wannan mukami ba. Bayani ku ka tambaye ni a rubuce, kuma ga shi nan na rubuto na damka maku.
“Duk abin da ku ka tambaya na yi bayani na yi, kuma a daidai lokutan da ku ka ce na yi bayanin abin da ya faru na yi bayani. To ba ni ne shugaban sojoji a lokacin ba.
“Batun cinikin makamai kuma wasu tsiraru ne su ka yi shi, tun kafin na hau shugabancn sojojin Najeriya. Za ku iya ku gayyace su ku titsiye su, domin su yi maku bayani kan wasu batutuwan da ke cikin wannan rahoto da na gabatar maku.
An kafa wannan kwamiti domin ya yi binciken yadda aka yi kwangilolin cinikin makamai da sauran kayayyakin sauran bangarorin jami’an tsaro, da su ka hada da ‘yan sanda da sauran bangarorin tsaron kasar nan.
PREMIUM TIMES HAUSA ta bada labarin cewa Kwamitin Bincike Ya Fara Farautar Manyan Hafsoshin Da Su Ka Yi Wa Kudin Makamai Luguden Wuta.
Ta byyana yadda Kwamitin Majalisar Tarayya da aka kafa domin ya binciki ikirarin da Mashawarcin Shugaba Muhammadu Buhati a Fannin Tsaro, Babagana Monguno ya yi cewa makudan kudaden da aka ware domin a sayo makamai a karkashin su Janar Mai Ritaya Tukar Buratai sun bace, kuma ba a sayo ko barkonon tsohuwa ba, ya gayyaci sabon Babban Hafsan Sojojin Najeriya, Janar Ibarahim Attahiru.
A ranar Litinin ce Attahiru ya bayyana a gaban kwamitin binciken, bayan a baya ya kasa bayyana a gayyatar farko da su ka fara yi masa har sau uku.
A ranar 22 Ga Maris ne dai aka gayyaci Attahiru wanda ba a lokacin sa aka salwantar da dala bilyan daya da Monguno ya yi zargi ba, aka gayyaci Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefile, amma duk ba su bayyana ba.
Haka ma a ranar 7 Ga Afrilu, an nemi su bayyana, amma ba su bayyana din ba.
Sai dai kuma a bayyanar da ya yi a ranar Litinin, Attahiru ya bayyana wa kwamitin bincike cewa ya kasa bayyana ne saboda wasu muhimman sha’anonin da su ka sha kan sa, wadanda kuma duk sun jibinci matsalolin tsaron kasar nan.
Sai dai kuma bai bada hakuri ba, inda ya ce bayanin da ya yi masu ya wadatar.